Mai kudin duniya Jeff Bezos ya isa duniyar wata
Tun ina dan shekara biyar nake mafarkin tafiya zuwa duniyar wata.
Attajirin da ya fi kowa kudi a doron kasa, Jeff Bezos tare da abokan aikinsa guda uku sun samu nasarar sauka a duniyar wata bayan tsawon shekaru 20 da aka dauka ana fafutukar ganin wannan rana.
A yau Talata, tsohon Shugaban kamfanin Amazon, da dan uwansa, Mark Bezos, da wata matukiyar jirgin sama Wally Funk tare da wani dalibin kasar, Holland Oliver Daemen, kumbonsu ya samu damar sauka a inda suka nufa.
Kamar dai yadda bayanai ke cewa kumbon da ya lula da su na da girma sosai, wanda kamfanin Bezos ya kera, karon farko da ya yi jigila zuwa sama jannati.
Jirgin wanda ya tashi daga Arewacin Texas da ke Amurka, ya yi tafiyar tsawan kilomita 100 kwatankwacin Mil 62, kafin ya tsallaka wata duniyar.
Kumbon dai na dauke da wata mata mai suna Funk ’yar shekaru 82 mafi tsufa da ta taba zuwa duniyar wata a tarihi, sai Daemen mai shekaru 18 wanda ya kasance mafi karancin shekaru da ya taba tsallake wannan duniyar.
Bezos ya dade da bayyana sha’awar zuwa wannan wuri, yana mai cewa labarin zuwa duniyar wata ya sauya rayuwarsa kuma ya bashi kwarin gwiwar neman zuwa wannan duniyar da ba tamu ba.
Tun a watan da ya gabata ne Aminiya ta ruwaito cewa, Jeff Bezos zai je duniyar wata a cikin kumbon farko mai dauke da mutane da dama wanda kamfaninsa na Blue Origin ya kera.
Bulaguron an tsara yin sa ne ranar 20 ga watan Yuli, kwana 15 kafin Jeff Bezos ya sauka daga mukamin Babban Jami’in Kamfanin Amazon.
Kamfanin Blue Origin ya ce kanin attajirin, Mark Bezos, shi ma zai shiga ayarin wan nasa zuwa duniyar watan a cikin kumbon mai suna New Shepard.
‘Tun ina karami nake mafarkin zuwa duniyar wata’
Bezos mai shekara 57, ya wallafa shafin Instagram cewa, “Tun ina dan shekara biyar nake mafarkin tafiya zuwa duniyar wata.
“A ranar 20 ga watan Yuli, zan yi wannan babban bulaguron tare da kanina kuma babban aminina.”
Bezos ya zama biloniya na farko da ya je duniyar wata
A yayin da a yanzu burinsa ya tabbata, Bezos ya zama biloniya na farko da ya zuba miliyoyin daloli a harkar tafiya zuwa duniyar wata ya kuma shiga kumbon da aka kera masa domin zuwa can.
Yawan dukiyar Mista Bezos, wanda shi ne ya fi kowa kudi a duniya, ta kai Dala biliyan 187 kuma ya kafa kmafanin Blue Origin ne a shekarar 2000.
Blue Origin ya gudanar da gwaje-gwaje fiye da 12 na aika kumbon amma ba tare kowa a cikinsa ba, daga inda kamfanin yake da zama a wani kauyen Jihar Texas.
Bayan shekara shida ana ta gwajin New Shepard cikin sirri, kamfanin Blue Origin ya sanar a watan Mayu cewa yana shirye-shiryen daukar fasinjoji a cikin kumbon zuwa duniyar wata.
Shi ma attajiri Elon Musk, wanda kamfaninsa na SpaceX ya kera manya-manyan kumbon da za su iya shawagi zuwa duniyar Orbit daga nan doron duniyarmu, ya sanar da shirinsa na yin bulaguron zuwa duniyar watan a cikin kumbon da kamfaninsa zai kera.
Attajirin ya kafa kamfanin Amazon a 1994 da Dala dubu 250 da ya samu daga iyayensa, da farko a zaman shagon sayar da littatafai ta intanet.
Ko bayan ya sauka daga shugabancin kamfanin na Amazon, Jeff Bezos, ba zai tsame hannunsa gaba daya daga harkokin kamfanin ba inda zai ci gaba da aiki a zaman Shugaban Zartarwar kamfanin.
Andy Jassy, wanda shi ne Shugaban harkokin intanet na kamfanin zai gaje shi a kujerar Babban Jami’in Kamfanin na Amazon.
Jeff Bezos ya ajiye aiki
Jeff Bezos ya ajiye aikinsa na shugabancin kamfanin Amazon da ke hada-hadar kayayyaki ta Intanet.
A ranar Litinin, 5 ga watan Yulin bana ne Andy Jassy ya maye gurbin Bezos, wanda ya kawo karshen zama shugaban kamfanin da ya shafe fiye da shekaru 20 yana jagorancinsa.
A shekarar 1994 Bezos ya kirkiri kamfanin na Amazon, inda ya fara sayar da littafai kafin ya habaka zuwa sayar da kayayyaki ta yanar gizo.
A yanzu alkaluma sun nuna kamfanin yana da darajar da ta haura Dala Tiriliyan 1.75.
Kamfanin ya samu riba mai tarin yawa a lokacin annobar Coronavirus, fiye da wacce ya samu a tarihi kasancewar mutane da dama na da bukatar kayayyaki da kuma ayyukan kamfanin.
Mujallar Forbes da ke fidda da alkaluma kan ababen da suka shafi rayuwar duniya, ta ce Bezos yana da dukiya da ta haura Dala biliyan 200.
Kafar labarai ta CNN ta ruwaito cewa, tun a watan Fabrairun da ya gabata ne kamfanin ya sanar cewa Bezos zai sauka daga mukaminsa.
Sai dai bayanai sun ce zai ci gaba da kasancewa yana da iko mai karfi a kansa.