Mai kula da Kabarin Manzon Allah (SAW) ya rasu
An yi jana’izar mai kula da dakin da kabarin Manzon Allah (SAW) yake a Masallacin Madina, Agha Abdou Ali Idris Sheikh
Allah Ya yi wa mutumin da ke kula da dakin da kabarin Manzon Allah (SAW) yake a Masallacin Madina, Agha Abdou Ali Idris Sheikh, rasuwa.
Agha Abdou Ali Idris Sheikh, daya ne daga cikin mutanen da suka fi dadewa suna hidima a Masallacin Manzon Allah (SAW) da ke Madina.
Hukumar Gudanarwar Masallatan Harami ta sanar cewa, Agha Abdou Ali Idris Sheikh, ya koma ga Mahaliccinsa ne a ranar Litinin.
An gudanar da Sallar Jana’izarsa a Masallacin Manzon Allah sannan aka kai shi makwancinsa na karshe a Makabartar Baki’ da ke Makwabtaka da Masallacin Madina.
- Ganduje ya yi alhinin rasuwar Darakta Aminu S. Bono
- Zaben Kano: Ba a ba mu kundin hukuncin kotun dukaka kara ba —NNPP
Abdou Ali Idris Sheikh shi ne Agha na uku da ya rasu cikin shekaru 10 da suka wuce.
A baya yawan masu aikin Agha ya haura mutum dubu daya, amma a halin yanzu wadanda suka rage a raye ba su fi biyar.