Mai kwarmin ido da wuri yake fara kuka

Shugaba Goodluck Jonathan ya fahimci cewa ta’asa da danyen aikin da shi da Ministocinsa suka tafka yayin gudanar da ayyukansu za su jefa su cikin matsananciyar walahar da za ta kai su shiga-uku bayan saukarsu.Saboda haka nan sai ya shawarce su da jan damara da kuma nuna juriya lokacin da aka takura masu don bin […]

Mai kwarmin ido da wuri yake fara kuka
Mai kwarmin ido da wuri yake fara kuka

Shugaba Goodluck Jonathan ya fahimci cewa ta’asa da danyen aikin da shi da Ministocinsa suka tafka yayin gudanar da ayyukansu za su jefa su cikin matsananciyar walahar da za ta kai su shiga-uku bayan saukarsu.Saboda haka nan sai ya shawarce su da jan damara da kuma nuna juriya lokacin da aka takura masu don bin bahasin wata kasassaba ko kuma take-takensu. 

Shugaba Jonatahna ya furta haka ne kuwa a wani Coci a Unguwar Life camp dake Abuja a ranar Lahadi lokacin da ya je can tare da uwargidansa, Dame Patience Jonathan, wacce tun bayan shan kayin zabe da mijinta ya yi ba a sake ganin fuskarta ba, domin ta daina halartar sha’ani da kuma bukukuwa. Shugaba Jonathan ya je ne yin sujadar ban-kwana da jama’a ganin cewa mulkinsa ya zo karshe, kuma saura ‘yan kwanaki ya zamo talaka futuk.
Shugaba Jonathan ya yi mamakin yadda jama’a suka guje masa, hatta na hannun damansa ma sun kama gabansu, ‘yan kadan ne, wadanda suka zame masa dole, ke tare da shi a halin yanzu. Da alama dai Shugaba Jonathan ya mance cewa duniya ba ta yi da ragon da aka kayar, sai jarumin da ya yi kaye. Saboda haka nan sai ya ce ba domin komai ne ba kuwa aka watse, aka rabu da shi, sai domin wani matakin da ya dauka, wanda kuma ya ki fayyace kowane irin mataki ne, kuma ya yi haka ne don amfanin daukacin ‘yan Najeriya, amma sai aka kasa fahimtar manufarsa, aka komo ana kyamarsa dangane da haka.
Ya nuna cewa ba safai jama’a suke fahimtar shugaba idan ya dauki mataki mafi alheri ga kowa ba, sai bayan ya bar mulki, kamar yadda wani tsohon Shugaban farar fata na karshe a Afrika ta Kudu, Mr de Clerk ya yi lokacin da ya yanke hukuncin kawo karshen mulkin ‘yan tsirarun fararen fatar kasar don mayar da mulki ga babbakun da ke da rinjaye. Ya ce a lokacin an yi masa caa, ana ta tsattsagarsa, kamar za a cinye shi danye, kuma hatta ma matarsa sai da ta kaurace masa. Ya ce to irin abin da ya faru gare shi ke nan a halin yanzu, kuma yana fata uwargidarsa, Patience wacce ta tafi bulaguro wata kasar Afrika bayan an tika shi da kasa a zaben shugabancin kasa ba za ta tsallake, ta bar shi ba bayan saukarsa daga mulki.
To akwai abin dubawa game da wannan furuci na Shugaba Jonathan, wanda ya saba yin jawabai masu daukan hankulan jama’a a coci. Ya bukaci mutanen da suka yi aiki tare da shi da su shirya shiga tasku domin kuwa wai a cewarsa sabuwar gwamnatin Janar Muhammadu Buhri za ta takura masu, ta hana su sakat, bayan saukarsu.Kuma hatta shi ma ba zai tsira ba. A, to, ai wanda ya ci buzu tilas ya yi aman gashi. Ba su ci nanin ba, sai nanin ta ci su?
Sai a yanzu ne Shugaba Jonathan zai san cewa bayan saukarsu mulki za a nemi bin bahasin ta’asar da suka tafka? Ya manta cewa akwai ranar kin dillanci, watau ranar da hajar Maigari ta bace? Babu wani abin da zai faru ga kowa sai dai girbin abin da ya shuka. Ayyukan wani Shugaba ko jami’in Gwamnati tamkar kwikuyo suke, ko ya bar aiki suna nan biye da shi. Idan na kirki ne ya mori abinsa, idan kuma na sharri ne ya gani da idanunsa. To shi ne tun ba a fita gari ba sai aka fara ihu, “Ga kura nan.” Babu wata alamar cewa za a kuntata wa kowa sai wanda ya muzgunawa jama’a muddin dai har ya wawushe dukiyarsu ko ya hana ruwan yi masu ayyukan alheri gudana. Irinsu ne za a kakkama, a tattatse abubuwan da suka hadidiya.
Talakawa jira suke wannan lokacin ya zo, domin kuwa har sun rigaya sun sanya wasu daga manyan jami’a gwamnatin Jonathan suna, “Igiya jike,” sun kuma yi wa janar Buhari lakanin “Dodon marasa gaskiya.” Ai bai kamata Shugaba Jonathan ya yi batun cewa za a kuntata masa shi da mutanensa ba. Ko ba komai ai yana sane da cewa irin wannan ranar za ta zagayo. Ya manta tozartawa da cin kashin da suka yi wa Janar Buhari irin wanda ba a taba yi wa wani dan siyasa irin haka ba a Nijeriya? Sun takura masa, sun muzguna masa, sun yi masa wulakancin da ko kare ba zai ci ba kafin zaben shugaban kasa, amma shi ko gezau, ya san cewa ba domin komai ba ne aka yi masa haka ba sai don tsayawa da ya yi kan gaskiya da kamanata adalci, kuma idan Allah ya kai shi ga biyar bukatarsa ta dankar ragamar mulki zai yi maganin zalunci, ya kafa adalci sa’anan ya kawar da ha’inci.
Talakawan Najeriya dai sun san cewa babu yadda za a yi wasu daga cikin manyan jami’an gwamnatin Shugaba Jonathan su tsallake siratsin gwamnatin Janar Buhari, domin ko ba a fada ba an san irin wadakar da aka yi da dukiyar jama’a, an kuma san wadanda suka yi ta tumumusarta, an kuma fahimci yadda wasu suka rika jidar ta, suna tsibewa a kasashen ketare, sai ka ce gadon kaka-da-kakanninsu. Janar Buhari dai bai da niyyar kuntata wa kowa kamar yadda Shugaba Jonathan ke hasashe, abin da kawai aka tabbatar zai yi shi ne gurfanar da wadanda suka sha, ta fi cikinsu a gaban alkalin da zai kuntata masu amayar da dukiyar haram din da suka zakalkala. Gwanayen magana dai suna cewa mai kwarmin ido tun da wuri yake fara kuka. Shugaba Jonathan ya san cewa ko ba dade, ko ba jima, gaskiya sai ta yi halinta, kuma tsuntsun da ya kirawo ruwa shi ruwan zai duka.