Mai laifin da ake nema ya zama kurman bogi na tsawon shekara 20

Bai taɓa tuntubar iyalinsa ba sama da shekara 10 da suka gabata, amma duk da haka sun yi nasarar gano shi.

Mai laifin da ake nema ya zama kurman bogi na tsawon shekara 20

Wani matashi dan kasar China mai suna Xiao da ake nema ruwa a jallo kan zargin kisa ya basar da ’yan sanda na tsawon sama da shekara 20 ta hanyar zama kamar kurma a tsaunukan Lardin Hubei.

A yammacin 22 ga watan Mayun 2004, matashi Xiao da aka ce yana da saurin fushi ya samu sabani da wani makwabcinsa a kauyensu Oumio Xaying, a Gundumar Diangcheng ta Jihar Xianyang.

A lokacin an ce Xiao ya ɗauki cebur ya buga wa makwabcinsa a kai, ya kashe shi nan take.

Kuma ganin zai fuskanci hukuncin ƙarasa sauran rayuwarsa a gidan kurkuku ko hukuncin kisa, sai Xiao ya yanke shawarar watsi da matarsa da ɗansa mai shekara 11 don tsira da ransa.

Ya gudu zuwa cikin tsaunukan Gundumar Andi, a Lardin Fujian, inda ya zama mai harkar sayar da gwangwan don dogaro da kai.

Don tabbatar da cewa bai taɓa ba da wani abu game da rayuwarsa ta baya ba, Xiao ya mayar da kansa kurma a tsawon shekara 20, sai dai kawai ya yi murmushi ga mutane da kuma sadarwa ta hanyar ishara.

Duk da tsawon lokacin ’yan sanda sun ci gaba da kokarin gano Xiao don gurfanar da shi a gaban shari’a, kuma duk da cewa ya gudu yana dabara, bai taɓa tuntubar iyalinsa ba sama da shekara 10 da suka gabata, amma duk da haka sun yi nasarar gano shi.

A watan jiya ne ’yan sandan birnin Andi suka kama wanda ke nuna alama kurma ne mai sana’ar gwangwan saboda zargin ya taɓa yin faɗa da wasu mutanen yankin.

Kuma duk da an sake shi jim kaɗan, an ci gaba da bincike kansa, kuma hotunansa sun karade tare da bayanansa a kasar baki daya.

A yayin da ake bankaɗo tsoffafin hotunan Xiao haɗe da waɗanda suke cikin kundin bayanan kasar, sai ’yan sandan suka samu hoto mai ban-mamaki da ya yi kama da wanda suke nema.

Wanda ya yi kama da kurman a Lardin Fujian da ake nema, don haka aka tura ’yan sanda don gudanar da bincike.

Da aka gano wanda ake zargin, sai suka tambaye shi, “Shin daga Gundumar Xiangcheng a Xianyang kake, nan take ya amsa da “Eh.” “Na shafe shekara 20 ina boye maganata, kuma na ji kamar na haukace,” in ji Xiao da ya saki jiki ga ’yan sanda.

Ya ce “Lokacin da na yi gudun kame, ɗana yana ɗan shekara 11, kuma yanzu sama da shekara 20, ina mamakin halin da iyalina suke ciki.”

Tun daga lokacin aka mayar da Xiao kauyensu, kuma duk da cewa ya daɗe yana tafiya, ya nuna musu gaskiyar inda ya yi rigima da alaƙarsa da makwabtansa a wancan yammaci.

Yanzu dai zai yi zaman gidan yarin da ya daɗe yana gudu.

Mutanen da suka san shi a matsayin kurma sun shaida wa ’yan sanda cewa ba su taɓa zarginsa da aikata laifin da yake gudu ba.

Ya ɓoye asalinsa bai taɓa magana da kowa ba, don haka babu wanda ya san komai game da shi.

Wannan labarin ya tuna da wani ɗan gudun hijira da aka yi rubutu game da shi a bara, wanda ya kwashe shekara 14 na rayuwarsa a ɓoye a cikin kogon dutse bayan ya yi wa gidan mai fashin Dala 23.

NLC ta yi watsi da ƙara kuɗin kiran waya da data

DSS ta gurfanar da Mahdi Shehu kan zargin ta’addanci

Sojoji sun kashe mataimakin Bello Turji

Harin ’Yan Fashi: Buni ya jajanta wa ’yan kasuwar Ngalda