Mai larurar tabin hankali ya tashi hankalin masu ibada a Masallacin Harami

Mahukunta a kasar Saudiyya, sun sanar da cewa wani mutum mai fama da larurar tabin hankali ya gigita masu ibada yayin da ya rika rusa ihu a cikin masallacin Harami na Makkah. Shafin Twitter na Haraimain Sharifain, masu lura da al’amuran da suka shafi masallatai biyu mafi daraja a doron kasa na Makka da Madina, […]

Mai larurar tabin hankali ya tashi hankalin masu ibada a Masallacin Harami

Masallacin Harami na Makkah

Mahukunta a kasar Saudiyya, sun sanar da cewa wani mutum mai fama da larurar tabin hankali ya gigita masu ibada yayin da ya rika rusa ihu a cikin masallacin Harami na Makkah.

Shafin Twitter na Haraimain Sharifain, masu lura da al’amuran da suka shafi masallatai biyu mafi daraja a doron kasa na Makka da Madina, shi ne ya wallafan da Yammacin ranar Alhamis.

Ihun  mai hade ta karaji na take da mutumin ya rika rusawa ya tayar da hankalin masu ibada tare da tsayar musu da ayyuka a cikin masallacin da ke birnin Makkah.

Sai dai ba tare da wata-wata ba jami’an tsaro suka fitar da shi daga cikin masallacin sannan suka muka shi ga jami’an ’yan sanda.

Aminiya ta ruwaito cewa, a makon jiya ne wata gobara ta tashi a wani gini da ke kusa da masallacin fiyayyen Halitta (SAW) a birnin Madinah.

Lakurawa sun kashe ma’aikatan kamfanin Airtel 3 a Kebbi

Matashi ya kashe mahaifiyarsa don yin tsafi a Kuros Riba

DSS ta ceto mutum 4 da aka sace a Sakkwato

2025: Wutar lantarkin Najeriya ta ɗauke gaba ɗaya