Mai laya kiyayi mai zamani
Batun da Bahaushe ke yi cewa baki ya san abin da zai fada, amma bai san amsar da za a mayar ba, ya tabbata kan Dokta Ahmed Abubakar Gumi don wasikun da ya rubuta wa tsohon shugababan kasa, Janar Muhammadu Buhari da kuma shugaban da ke bisa karagar mulki, Dokta Ebele Jonathan, ganin irin raddin […]
Batun da Bahaushe ke yi cewa baki ya san abin da zai fada, amma bai san amsar da za a mayar ba, ya tabbata kan Dokta Ahmed Abubakar Gumi don wasikun da ya rubuta wa tsohon shugababan kasa, Janar Muhammadu Buhari da kuma shugaban da ke bisa karagar mulki, Dokta Ebele Jonathan, ganin irin raddin da aka mayar masa daga kowane bangaren kasar nan. Shi dai Dokta Ahmed Gumi haka nan da rana tsaka, zikau-mikau, ya dauki alkalaminsa don rubuta abin da yake gani shawara ce ga wadancan hamshakan ‘yan siyasa guda biyu bisa al’amarin da bai shafi addini ba.
Ya bukaci Janar Muhammadu Buhari da kuma Dokta Ebele Jonathan da su janye fafitikarsu ta tsayawa takara, domin kuwa hakan na tattare da mummunar hadari ga kasar da kuma al’ummomin cikinta, domin a ganinsa nasarar kowanne daga cikinsu na iya tayar da gagarumar rigimar da za ta iya kone kasar kurmus. Wannan al’amari ne da ya rataya bisa wuyar gwamnatin da za ta tabbatar da cewa an yi zabe mai inganci don a zauna lafiya.
A daidai lokacin da Dokta Gumi ya kattaba waccan wasikar, magoya bayan Janar Muhammadu Buhari sun soki lamirin batutuwan da ta kunsa, musamman ma saboda dai babu wanda ya nemi irin wannan shawarar daga gare shi, kuma idan ba da niyyar tujara ko tozartawa ya yi ta ba, me ya hana shi ganawa da Janar Buhari cikin sirri, ya yi masa nasiha, kamar yadda addinin Musulunci ya bukaci a yi wa juna. A’a, a wajen Dokta Gumi wannan ba komai ba ne domin ya dade da yin amanna cewa akwai wadanda suke matukar bukatar ganin daya daga cikin wadancan mutanen biyu ya janye daga takara, shi ya sa ya yi musu susa inda ke masu kaikayi. Saboda haka me zai hana shi furta irin wadancan lafuzzan ko da kuwa hakan ba zai yi wa wasu dadi ba? To ana iya cewa da gangan ke nan Dokta Gumi ya rubuta waccan wasikar don ya dadadawa wadanda ke son ganin lallai sai Janar Buhari ya janye daga fagen siyasar, ya bar wandanda za su cutar da jama’ansa.
Sanin kowa ne makiya zaman lafiya a kasar nan sun sha yin kokarin ganin bayan Janar Buhari ta hanyar yi masa batancin da zai bakanta shi a idanun ‘yan Najeriya. Sun yi masa zargin amfani da addini a siyasa, alhali kuwa su ne suka mayar da addinin makamin yakarsa. An nemi a aika da shi barzahu don kada ya hana su taka rawar gaban hantsi yayin zaben watan Fabrairun badi, amma ta Allah ba ta su ba, sai ga shi nan Allah Ya tserar da shi, ya kuma ci gaba da bin manufarsa ta fitar da kasar nan daga kangin azzaluman da suka hana ta kai wa ga kasaita.
To a sabili da hakarsu ta halaka Buhari ba ta cimma ruwa ba, sai aka kara ci gaba da batun addini don halaka shi. A wanan karon sai aka hada da wasu malaman addininsa don a yaudare shi, a hana shi amfani da hakkinsa na dan kasa don taimakon jama’ar da aka mayar tamkar bayi marasa galihu a kasar haihuwarsu. Akwai abin da ya fi haka ban takaici, a ce ana amfani da naka don a kai ka kasa? Talakawan Najeriya, musaman ma na Arewa na sane da cewa hanyar jirgi dabam ta mota kuma dabam, matsayin siyasa a al’amuran rayuwar jama’a dabam, haka nan ma addini akwai nasa wuri na dabam a kokarin nesantar da jama’a daga abin da zai raba su da imaninsu kafin komawarsu ga Mahaliccinsu.
To sa’ilin da Dokta Gumi ya dage lallai sai su Buhari sun yi aiki da nasiharsa, an yi ta nuna masa rashin dacewar haka, amma sai ya yi biris da masu fadakar da shi game da rashin dacewar nacewarsa,amma sai shi ma kansa ya mayar da nasihar wasu a wurinsa ba a bakin komai ba. An nuna masa haka ne don ya fahimci cewa zakewarsa cikin sha’anunuwan siyasa na iya janyo masa bakin jini, domin siyasa ta rigaya ta rarraba kawunan jama’a, kuma wasu na iya yi wa batunsa muguwar fahimta.
Iallai kuwa hakan ya faru, domin dai Dokta Gumi ya bukaci Janar Buhari ne da Ebele Jonathan da kada su tsaya takara, amma sai ga shi nan a ranar Asabar din makon jiya wasu manyan jaridun Yammaci da Gabashin kasar nan sun wallafa batun waccan wasikar a shafukkansu na farko baro-baro, sa’anan kuma suka yi makircin da suka saba don nuna cewa Dokta Gumi ya nemi Dokta Ebele Jonathan ne shi kadai da kada ya kuskura, ya tsaya takara, saboda kasancewarsa ma’abucin rarraba kawunan jama’a, amma ba su nuna cewa ya rubutawa janar Buhari irin waccan wasikar ba. Dalilinsu na yin haka kuwa shi ne cewa al’ummar Arewa ne ba su kaunar tsayawar Jonathan takarar shugabancin kasar nan.
Wannan ba sabon abu ba ne, domin kuwa ya dace da take-taken Yahudu da Nasara na kokarin ganin sun dakile yunkurin wasu jinsin kasar, ba domin komai ba sai don abin da suka yi imani da shi. To shi Dokta Ahmed Gumi bai sara ne yana duban bakin gatari? Ai wannan wasikar tasa wasu da yawa sun dauka surkulle ce kawai, kuma soki burutsu, domin kuwa bakin alkalami ya bushe. Shi Jonathan din da yake nema ya janye, ai ya fito takarar da karfinsa, ya kuma rungumi shugaban kungiyar addininsa zuwa kasar Yahudu don aikin ibada. To me zai hana shi Dokta Gumi ba zai kusanci nasa gogan ba, sai ya dage, yana neman kwashe masa kafafu? To fa a wannan al’amari tilas ne mai laya ya kiyayi mai zamani.