Mai magana da yawun Tinubu, Ajuri Ngelale ya ajiye aiki
Ngelale ya buƙaci a ba shi dama ya gudanar da harkokin da ke gabansa a yanzu cikin sirri.
Mai magana da yawun Shugaban Nijeriya, Ajuri Ngelale ya sanar da ajiye aikinsa ‘na wucin gadi.’
Mista Ngelale ya sanar da hakan ne cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Ngelale ya ce a ranar Juma’a ya miƙa takarda zuwa ga shugaban ma’aikata na fadar shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila domin sanar da shi aniyarsa ta tafiya hutun da bai san lokacin ƙarewarsa ba.
Ya bayyana cewa zai ajiye aikin ne domin mayar da hankali kan rashin lafiyar wasu iyalansa da bai bayyana ba.
“Na yi hakan ne domin samun isasshen hutun da zai ba ni damar mayar da hankalina kan matsalolin rashin lafiya da a yanzu haka iyalaina ke fuskanta,” in ji Ngelale.
Mista Ngelale ya kuma ce ya jingine duka sauran muƙaman da yake riƙe, da suka haɗar da wakilin Shugaban Kasa na musammman kan sauyin yanayi da kuma Shugaban Kwamitin shugaban ƙasa kan inganta muhalli.
“Na ɗauki wannan mataki ne bayan shafe kwanaki ina tuntuɓar iyalai da dangi kan yanayin rashin lafiya da ake fuskanta a gidanmu”, in ji shi.
Ya ce yana sa ran dawowa domin ci gaba da aikinsa, idan lokaci da rabo sun ba shi damar hakan.
Daga ƙarshe ya buƙaci a ba shi dama ya gudanar da harkokin da ke gabansa a yanzu cikin sirri ba tare da neman ƙarin bayani ba.