Mai martaba Maigwari ya yi magana saura gwamnatoci
“Na taba cewa mu a nan muna zaune cikin ukuba. Duk wasu ayyukan ci gaba da raya kasa da dukan abubuwa masu kyau da ake so a yi wa Birnin Gwari, ’yan ta’adda sun hana a yi su. Muna shan wahala, hatta gwamnati ba ta son ta zo inda muke.” Wadannan kalamai na cikin kalaman […]
“Na taba cewa mu a nan muna zaune cikin ukuba. Duk wasu ayyukan ci gaba da raya kasa da dukan abubuwa masu kyau da ake so a yi wa Birnin Gwari, ’yan ta’adda sun hana a yi su. Muna shan wahala, hatta gwamnati ba ta son ta zo inda muke.” Wadannan kalamai na cikin kalaman da Mai martaba Sarkin Birnin Gwari da ke cikin Jihar Kaduna, Alhaji Zubairu Jibril Maigwari ya furta a ganawar da ya yi da jaridar Daily Trust ta ranar Lahadi 31-03-2018, kan annobar ’yan ta’adda da masauratarsa ta dade tana fama da ita. Ta’addancin da yake haddasa kai hare-haren da suke jawo asarar rayuka da jikkata jama’a da sace dukiyoyinsu da yin garkuwa da mutane don neman kudin fansa a kusan dukan masarautar Birnin Gwari, kamar yadda ake fama da su a jihohin Zamfara da Katsina da suke makwabtaka da Jihar Kaduna da wasu jihohin kasar nan. Kanun hirar shi ne “Abin da ya sa na fada wa mutanena su kare kansu.”
Sarkin Birnin Gwari wanda ya dauko tarihin faruwar wannan ta’addanci a masarautartasa tun daga 1995 zuwa yau da lamarin ke ta fantsama da kara kazancewa, ya dora alhakin ci gaba faruwar hakan, a kan rashin kyan hanyar da ta tashi daga Birnin Gwari zuwa Kaduna da kasungurmin dajin da suke da shi da ya shiga cikin jihohin Zamfara da Katsina, ya fada Jamhuriyar Nijar. Ya kuma ce da rashin tura tsayayyu kuma jajirtattun jami’an tsaro na soja da za su fuskanci maharan. Ya yi nuni da yadda aka taba kawo musu wadansu zakakuran sojoji da suka yi aiki tukuru suka samu kame wadansu daga cikin wadanda ake tuhuma, suka tabbatar da an hukunta su. Kuma a fadarsa wadancan sojoji ba su dade ba, sai aka kwashe su, wadda ya ce ta yi matukar mayar da hannun agogo baya a yakin da ake da ’yan ta’addan a masarautartarsa.
A bisa kashe-kashen da ake yi a masarautartasa Alhaji Zubairu Maigwari ya ce a takaice a ’yan watannin nan an kashe mutum 64, kuma Allah kadai Ya san yawan wadanda aka sace aka yi garkuwa da su don neman kudin fansa a masarautar. Ya ce ’yan ta’addan sun yi karfin da za su iya kai farmaki ga sojojin da ke yankin, inda a kwanan nan a irin wannan farmaki suka kashe sojoji 11, wadanda aka yi jana’izarsu a Kaduna a makon jiya. Ya ce idan ’yan ta’addan za su iya tunkarar sojoji masu manyan makamai su yi mummunar barna irin waccan, to ina ga kauye ko kauyukan da mutanensu ba su wuce 200 ba.
Daga irin hoton Mai martaba Maigwari da aka dauko a lokacin hirar da irin amsoshin da ya rika bayarwa, sun nuna a cikin damuwa da bacin rai yake kan annobar da take samun masarautarsa shekaru aru-aru. Misali a tambayar da aka nemi jin irin yadda yake ji daga talakawansa, ko wane fanni na zamantakewa da tattalin arzikinsu ya fi shafuwa daga hare-haren ’yan ta’addan? Sai Sarkin ya amsa da cewa: “Kowane bangare na rayuwana addini ne, siyasa ce, tattakin arziki ne, duk yana samun koma baya. In ban da ma mutanenmu jajirtattu ne da tuni tattalin arzikinmu ya fadi warwas. Da a ce a jiya kazo ranar babbar kasuwarmu da ka ga yadda mutane suke ta kai-komo duk da rashin tsaron da muke fama da shi.”
Ya kuma koka kan yadda Shugaban kasa Muhammadu Buhari tun da ake wadannan hare-hare da kashe rayukan jama’a, bai taba sa kafarsa a Masarautar Birnin Gwari da nufin jaje ko ta’aziyya ba, bare ya duba irin barnar da aka yi, alhali sun ji ya je Zamfara sau biyu, baya ga jihohin Binuwai da Taraba da ya halarta inda su ma suke fama da irin wannan annoba ta ta’addanci, alhali jihohin da ya ce barnarsu ba fin munin ta Birnin Gwari ta yi ba. Hatta Gwamnan Jihar Malam Nasiru El-Rufa’i, inji Sarkin, bisa ga irin yadda ya ga ta’addancin da kashe-kashe a masarautar suna kara munana, har alkawari ya taba yi na zai dawo da ofishinsa Birnin Gwari, amma mai yiwuwa Gwamnan da Sarkin ya yaba masa a kan kokarin da yake na yaki da ta’addanci a yankin, shi ma ya gundure shi.
Mai karatu kada ya ce kalaman na Maigwari za su iya zama daya da wanda tsohon Babban Hafsan Sojojin kasa kuma tsohon Ministan tsaro Laftana Janar Theophilus Yakubu danjuma ya yi a ranar 24-03-2018, a wajen bikin yaye daliban Jam’iar Jihar Taraba (jiharsa) a garin Wukari, inda aka rawaito Janar din yana zargin akwai niyyar kakkabe wata kabila a jihar da wasu jihohi da suke bakin koguna da yankunan karkarar kasar nan, har ma yake cewa: “Dole mu hana. Dole mu tsayar da ita. Kowannenmu sai ya tashi tsaye.” Kuma ya ci gaba da cewa, “Sojojinmu sun kasa zama ’yan ba-ruwanmu, sun zama suna daukar bangare, suna hada baki da ’yan ta’adda masu makamai suna kashe mutane suna kashe ’yan Najeriya. Muddin kuna dogaro da sojoji a kan za su iya hana kashe-kashen, duk za ku mutu daya bayan daya.”
Idan ka yi la’akari da kalaman manyan mutanen biyu, za ka ga cewa kowanensu a fusace yake bisa halin da mutanensa suke ciki da irin wadannan hare-haren ’yan ta’adda da suke kokarin game kasa. Amma kuma ya ci a ce Janar danjuma wanda nesa ba kusa ba ya fi Sarkin Birnin Gwari sanin yadda aikin soja yake, wanda tarbiyyarsu ita ce kishin kasa da son ta kafin nuna wani bambanci a kan jinsi, kabila ko addini, bayan kasancewar rayuwarsa gaba daya soja ya yi, har ya kai Janar kuma Babban Hafsan Sojojin kasa, kuma ya zama Ministan Tsaro. Dadin-dadawa Janar danjuma ya fi Mai martaba Sarkin Birnin Gwari ikon fada a ji a cikin harkokin tafiyar da kasar nan, wanda aka iya cewa duk wani wanda ke kan karagar mulki a yau, to kuwa yana girmama Janar danjuma bisa ga irin madafun iko da arzikin da Allah Ya ba shi. To yanzu me Janar danjuma zai ce a kan sojoji 11 da aka kashe a dajin Birnin Gwari, kin ba da hadin kai suka yi ga ’yan ta’addan yankin? Ya kamata dai mutane irin su Janar danjuma idan ba so suke su koma shugabannin tsirarin kabilun su ba, to su rika sanin abin da za su furta a kan rikicin kasar nan, musamman kasancewar yana da karfin fada a ji a kasar nan da ma duniya baki daya.
Ga Mai martaba Sarkin Birnin Gwari kuwa lallai akwai matukar damuwa tare da shi, ganin yadda ake kassara masarautarsa, don haka akwai bukatar mahukunta su kara damara wajen kawo karshen wannan annoba a ko’ina cikin fadin kasar nan.