Mai motocin Ferrari ne ya ‘dawo’ duniya a matsayin dan kwallo Ozil Mesut?

Sai dai mutanen biyu ba su taba ganin juna ba, hasali ma sai da Ferari ya rasu da wata biyu sannan aka haifi Ozil.

Mai motocin Ferrari ne ya ‘dawo’ duniya a matsayin dan kwallo Ozil Mesut?

Shin da gaske ne mutumin da ya mutu yana iya dowawa duniya a wani wuri ko wata kasa ya yi wata rayuwa ta daban?

Wannan ita ce tambayar da mutane da yawa ke neman amsarta yayin da hoton mutumin da ya kirkiri motocin alfarmar na tsere Enzo Ferrari da kuma fitaccen dan kwallon kafa Ozil Mesut suka bayyana, kai ka ce Danjuma ne da Danjummai ko Hasan ne da Husaini masu kama daya.

Sai dai an haifi Enzo Ferrari ne a ranar 18 ga watan Fabrairun1898 a garin Moderna ta kasar Italiya ya kuma tafiyar da rayuwarsa kacokam a harkar motocin tsere da na alfarma masu gudu inda motocinsa suka shahara a duniyar tseren motoci har zuwa tsakiyar Karni na 20.

Ya rasu a ranar 14 ga watan Agustan 1988 yana da shekara 90. Yayin da Ozil kuwa aka haife shi a ranar 15 ga watan Oktoban 1988 (kwana 60 bayan rasuwar Ferrari) a garin Gelsenkrchen na Kudancin Rhine – Westphalia a Jamus.

Asalinsa iyayensa sun yi gudun hijira ne daga kasar Turkiyya, ya kuma soma buga kwallo yana matashi inda ya yi fice lokacin da ya buga wa manyan kungiyoyi a Jamus da Ingila.

Matashin ya yi suna da fice a kwallon kafa inda yake bugun wasan tsakiya kafin ya yi ritaya a farkon shekarar 2023. Kamannin Ozil da Ferari ya kai matuka.

Ya isa a ce ciki daya suka fito kuma a matsayin tagwaye. Sai dai mutanen biyu ba su taba ganin juna ba, hasali ma sai da Ferrari ya rasu da wata biyu sannan aka haifi Ozil a 1988.

Shin da gaske Ferrari ne ya dawo duniya don sake wata rayuwar? Sai dai Bahaushe ya gama magana da cewa “kama da wane, ba ta wane.”

A ƙofar banɗakin Gidan Yarin Kuje nake kwana — Ɗan zanga-zanga

An ceto jaririyar da ’yar aikin gida ta sace a Edo

An ceto mutum 58 da aka sace a Kaduna

Sarkin Zazzau ya naɗa sabbin hakimai 7