Mai neman Shugabancin Amurka ya nisanta kansa da mahaifinsa

Tsohon gwamnan Jihar Florida Jeb Bush wanda yake kani ne ga tsohon Shugaban kasar Amurka George Bush kuma da ga George H W Bush, ya ce a daina danganta shi da wadannan mutanen biyu. Tsohon gwamnan ya yi jawabin game da manufofinsa kan kasashen waje wanda ke nuna cewa yana da muradin tsayawa takarar Shugaban […]

Mai neman Shugabancin Amurka ya nisanta kansa da mahaifinsa
Mai neman Shugabancin Amurka ya nisanta kansa da mahaifinsa

Tsohon gwamnan Jihar Florida Jeb Bush wanda yake kani ne ga tsohon Shugaban kasar Amurka George Bush kuma da ga George H W Bush, ya ce a daina danganta shi da wadannan mutanen biyu.

Tsohon gwamnan ya yi jawabin game da manufofinsa kan kasashen waje wanda ke nuna cewa yana da muradin tsayawa takarar Shugaban kasar Amurka a zaben shekarar 2016. Ya kuma caccaki manufofin gwamnatin Barack Obama, da kuma nisanta kansa da manufofi irin na maihaifinsa da na yayansa wadanda sun shugabanci kasar a wani lokaci a baya.
Ya ce: “Duk da yake na yaba da irin matakan da suka dauka a wasu batutuwa da ke da sarkakiya”. Har ila yau, ya suki lamirin wasu manufofin gwamnatocinsu domin a ganin sa sun saba wa tunaninsa.
Mista Jeb ya ba da misalin da sunayen mutanen da suka riki mukamai a gwamnatocin mahaifin nasa da yayansa. Ya ce “da yawan su idan ka dora su bisa sikili sai ka taras akwai rauni da yawa akan abubuwa da dama da suka aiwatar idan ka kwatanta shi da tarihi.”
To sai dai abin da wasu Amurkawa ke cewa shi ne duk yadda yas o ya nisanta kansa da mahaifin sa ko kuma yayansa har kullun zamowar su shugabanni kasar a lokutta daban daban a kasar zaiyi tasiri a zamar sa shugaban kasa ko kuma akasin haka.
Amma wasu Amurkawan ma cewa suka yi nisanta kansa da ’yan uwansa dabara ce domin hakan ba zai haifar masa da da mai ido ba.