Mai neman takarar Gwamnan Gombe ya goyi bayan ’yar tinke a zaben fid da gwani
daya daga cikin masu neman tsaywa takarar Gwamna su 7 a Jam’iyyar APC a Jihar Gombe Alhaji Abubakar Habu Mu’azu ya ce yana goyon bayan ’yar tike wato kato bayan kato a zaben fitar da ’yan takara don shiga zaben badi. Alhaji Habu Mu’azu, ya bayyana haka ne a ranar Lahadin da ta gabata a […]

daya daga cikin masu neman tsaywa takarar Gwamna su 7 a Jam’iyyar APC a Jihar Gombe Alhaji Abubakar Habu Mu’azu ya ce yana goyon bayan ’yar tike wato kato bayan kato a zaben fitar da ’yan takara don shiga zaben badi.
Alhaji Habu Mu’azu, ya bayyana haka ne a ranar Lahadin da ta gabata a lokacin da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan ziyarar da ya kai Sakatariyar Jam’iyyar APC ta Jihar don fara neman goyon baya a zaben na badi.
Ya ce a matsayinsa na mai son tsayawa takara yana neman hadin kai da goyon bayan duk dan Jihar Gombe ba lailai sai dan jam’iyyarsu ta APC ba, saboda dan jam’iyyarsa kadai ba zai zabe shi ya zama Gwamna ba.
Mai neman tsayawa takarar Gwamnan ya ce a lokacin da ya fito don zagaya gari akwai kungiyoyi fiye da dari da suka mara masa baya da nuna goyon bayansu gare shi. Abubakar Habu Mu’azu, ya ce duk da yana goyon bayan tsarin na ’yar tike da za a yi a zaben Shugaban kasa ya ce yana da kyau a yi amfani da tsarin a zaben fid da dan takarar Gwamna, amma kuma sai sauran ’yan takara da shugabanin jam’iyyar sun amince.
Da yake bayyana ayyukan madalla da ya yi wa al’ummar kauyuka a jihar ya ce a gundumomi 114 da ake da su a Jihar Gombe, babu gundumar da bai yi musu rijiyar burtsatse biyu zuwa uku ba, hakan ya sa ya zama daban da sauran ’yan takarar. Sai ya ce duk lokacin da ya fita kamfe yana da abin da zai fada da ya yi ga mutane don a zabe shi kuma idan ya zama Gwamna zai ninka a kai.