Mai neman takarar Shugaban Kasa a APC, Adamu Garba ya fice daga jam’iyyar
Ya ce sam jam’iyyar ba ta bin tafarkin Dimokuradiyya
Daya daga cikin masu neman takarar Shugabancin Najeriya a karkashin jam’iyyar APC mai mulki, Adamu Garba, ya sanar da ficewa daga jam’iyyar.
Adamu, wanda a ranar Laraba ya sanar da janyewarsa daga takara a jam’iyyar a zaben 2023 mai zuwa, ya ce jam’iyyar sam ba ta bin tafarkin Dimokuradiyya.
Ya sanar da hakan ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook da yammacin Juma’a.
Ya ce, “A matsayina na matashin da ya yi amanna da makomar Najeriya, ba zai yiwu na ci gaba da zama a cikin jam’iyyar da ke fifita kudi a kan cancanta ba.
“A zahirin gaskiya, bana tunanin akwai wani matashin da ke kaunar Najeriya yana da makoma a APC, na yi amanna jam’iyyar ta rusa turakun da aka kafata da su na Dimokuradiyya.
“APC ta gaza cika kusa dukkan alkawuran da ta daukar wa ’yan Najeriya, kai har gwara PDP ma da ita,” inji Adamu Garba.