Mai Pataskum ya buɗe masallacin garin Danga a Yobe
Ya yaba wa kasar Malaysia kan taka rawar gani wajen ciyar da addinin musulunci gaba a faɗin duniya.

Mai martaba Mai Pataskum, Alhaji Umaru Bubaram Ibn Wuriwa Bauya, ya jagoranci bikin buɗe sabon masallacin Juma’a da aka gina a Garin Danga a Ƙaramar Hukumar Potiskum da ke Jihar Yobe.
Bikin kaddamar da sabon masallacin Juma’ar, wanda ya jawo shugabannin al’umma, malaman addini, da mazauna yankin ya nuna irin gagarumin ci gaba da aka samu a harkokin addinin musulunci a yankin.
Mai Pataskum, wanda ya yi fice wajen bayar da gudunmawa wajen samar da zaman lafiya da ci gaba a yankin, ya yaba da kokarin da masu bayar da tallafi na kasar Malaysia suka yi na gina masallacin, tare da jaddada rawar da yake takawa wajen samar da haɗin kai da ci gaban yankinbmasarautar.
Mai martaba Sarkin ya yi addu’ar fatan alheri ga al’ummar masarautar, jihar Yobe da ma kasa baki ɗaya.
Ya kuma yaba wa yadda kasar ta Malaysia ke taka rawar gani wajen ciyar da addinin musulunci gaba a faɗin duniya.