Mai POS ya mayar da N10m da kwastoma ya yi kuskuren tura masa a Kano

An yaba da kyakkyawan halin mai POS ɗin kuma an buƙaci sauran jama’a da su yi koyi da shi.

Mai POS ya mayar da N10m da kwastoma ya yi kuskuren tura masa a Kano

Mai POS ɗin da ya mayar da kusan naira miliyan 10 da kwastoma ya yi kuskuren tura masa

Wani mai sana’ar POS a Unguwar Kurnar Asabe da ke Jihar Kano ya mayar da kusan naira miliyan 10 da wani kwastomansa ya yi kuskuren tura masa.

Lamarin dai ya faru ne yayin da kwastoman ya yi yunkurin tura wa mai POS din naira dubu 10, kamar yadda rundanar ’yan sanda Kanon ta bayyana a wata sanarwa da ta fitar ranar Alhamis.

Rundunar ta ce lamarin ya faru ne tun a watan Disamba na shekarar 2023, lokacin da mai sana’ar POS mai suna Mohammed Sani Abdulrahman ya fahimci cewa wani kwastomansa wanda ya karɓi naira dubu 10 daga wurinsa ya tura masa naira miliyan 10 bisa kuskure.

Daga nan ne sai mai POS ɗin mai shekaru 37 ya garzaya hedikwatar ’yan sandan Kanon ya sanar da su abin da ya faru.

Sai dai ’yan sandan sun ɗauki bayanansa kuma suka buƙaci ya ba su lokaci su gudanar da bincike don gano mutumin da ya tura masa maƙudan kuɗin bisa kuskure.

Sanarwar da Abdullahi Haruna Kiyawa, kakakin rundunar ’yan sandan ya fitar ta ce sun kwashe kimanin wata uku suna bincike kafin su gano mutumin wanda ɗan kasuwa ne a Kasuwar Dawanau da ke Kano.

Rundunar ’yan sandan ta ce tuni mai POS ɗin ya mayar wa kwastoman kuɗinsa wato naira miliyan tara da dubu dari tara da casa’in (9,990,000:00).

Sai dai jin daɗin haka ya sa ɗan kasuwar ya ba mai POS ɗin kyautar naira 500,000.

Kazalika rundunar ’yan sandan ta yaba da kyakkyawan halin mai POS ɗin kuma ta buƙaci sauran jama’a da su yi koyi da shi.