Mai PoS ya shiga hannu kan kashe N280m da aka tura masa bisa kuskure
Wani mai sana’ar kudi ta PoS ya shiga hannu bayan da ya kashe Naira miliyan 280 da aka yi kuskuren tura masa ta banki
Wani mai sana’ar kudi ta PoS ya shiga hannu bayan da ya kashe Naira miliyan 280 da aka yi kuskuren tura masa ta banki.
Matashin ya yi gaban kansa da kudin, inda ya biya wa mutane kujerun Umara da aikin Hajji, ya sayi motoci da gidade.
Wani wanda ke da masaniyar abin da ya faru ya ce mai PoS din, wanda dan unguwar Abayawo da ke Karamar Hukumar Ilori ta Arewa a Jihar Kwara, ya ce, “Matashin ya yi ta samun alat har na miliyan 280, da bai san ta inda suka fito ba, a ’yan makonnin da suka gabata.
“Maimakon ya ja hankalin bankin, sai ya shiga kashe kudin, ya sayi gidaje da motoci ya biya wa mutane kujerar Umara da aikkin Hajji; Yanzu haka wasu daga cikin wadanda ya biya wa Umara suna Saudiyyya ba su dawo ba tukuna.
“Duk da cewa ya kyautata wa ’yan unguwa amma jama’a sun yi ta mamakin yadda dare daya aka wayi gari mai harkar PoS ya zama wani hamshakin mai kudi.”
Majiyar ta ce a halin yanzu mai PoS din da ake zargi yana tsare a hannun ’yan sanda bayan sun zo da jami’an banki sun kama shi.
Aminiya ta ziyarci shagon PoS din wanda ake zargin, amma ta same shi a rufe; amma ’yan unguwar sun shaida wa wakilinmu cewa ya yi bulaguro ne, amma ba su san lokacin da zai dawo ba.
Kakakin ’yan sandan jihar Kwara, Ajayi Okasanmi (SP), ya ce daga sashen binciken manyan laifuka na hedikwatar ’yan sanda ta kasa aka je aka tsare matashin, “don haka ba mu da hurumin yin magana a kai.”