Mai rukiyya

Wani mai rukiyya ne zai cire wa wata aljani. Da ya zaunar da ita, aka rike ta. Bayan ya karanto ayoyi masu zafi, sai aljanin ya ce: ‘’Wayyo, kana kona ni.’’ Malamin ya ce: ‘’To me ya sa ka shiga jikinta?’’ Aljanin ya ce: ‘’Zan taimake ta ne.’’ Malam ya ce: “Wane irin taimako bayan […]

Mai rukiyya
Mai rukiyya

Wani mai rukiyya ne zai cire wa wata aljani. Da ya zaunar da ita, aka rike ta. Bayan ya karanto ayoyi masu zafi, sai aljanin ya ce: ‘’Wayyo, kana kona ni.’’ Malamin ya ce: ‘’To me ya sa ka shiga jikinta?’’ Aljanin ya ce: ‘’Zan taimake ta ne.’’ Malam ya ce: “Wane irin taimako bayan cutar da ita kake yi?’’ Aljani ya ce: “Ina so in taimaka mata ne, domin ta ci gasar Naira miliyan ashirin na MTN (Who Want To Be A Millonaire).” Da malamin ya ji haka, sai ya yi kasa kasa da murya ya ce: ‘’To fita daga jikinta ka dawo jikina.”

Daga Bashir Rabiu Mudi, 07030058300