Mai satar yara a majami’u ya shiga hannu a Legas
Jami’an tsaro na farin kaya sun yi nasarar damke Gabriel Ogunsawe, daya ne daga cikin gungun bata garin da ke garkuwa da kananan yara a majami’u domin amsar kudin fansa. A ta bakin Ogunsawe, dan kimanin shekara 26, wanda a halin yazu yake tsare a kurkukun jami’an tsaron na farin kaya da ke a Panti-Yaba, […]
Jami’an tsaro na farin kaya sun yi nasarar damke Gabriel Ogunsawe, daya ne daga cikin gungun bata garin da ke garkuwa da kananan yara a majami’u domin amsar kudin fansa.
A ta bakin Ogunsawe, dan kimanin shekara 26, wanda a halin yazu yake tsare a kurkukun jami’an tsaron na farin kaya da ke a Panti-Yaba, Legas, ya aikata yin garkuwa da kananan yara har a sau uku, a inda suka samu nasara da farko amma dubunsu ta cika a yunkurinsu na biyu da na uku, inda jami’an tsaro suka yi sa’ar cafke shi tare da gurfanar da shi gaban shari’a; inda aka daure shi na kusan shekara daya a kurkukun Kiri-kiri da ke Ikko. Bayan sako shi ne ya kara komawa gidan jiya kuma aka kama shi.
“Ni dan asalin Ijebu Ode ne a Jihar Ogun, na yi karatun diploma a Kwalejin Fasaha ta Jihar Legas. An kama ni sakamakon kasancewata daya daga gungun da suka yi garkuwa da yaro dan shekara hudu a majami’ar Grace da ke a Palmgrobe a Legas. Abokina Olayinka ne ya sanya ni cikin wannan mugunyar sana’a.” Inji mai laifin a yayin da yake bayani ga jami’an tsaron.
Ya kara da cewa: “Mun kasance muna aiwatar da garkuwar ne kamar haka: Olayinka kan ziyarci duk majami’ar da zuciyarsa ta raya masa a safiyar Lahadi, ya yi zaune tamkar memba ne a majami’ar, kana ya yi lamo yana bibiyar shige da ficen masu bauta a majami’ar. Da zarar ya samu damar fita da yaro ba tare da an lura da shi ba, sai ya yi hakan ta hanyar yaudarar yaron da biskit ko kayan wasan yara, daga nan sai ya sake zuwa wata majamiar nesa da ta farko.”
“Ba mu kisa ko sayar da yaran da muke garkuwa da su, mukan tabbatar mun karbi kudin fansa kafin mu sake su. Mukan boye su na tsawon kwana guda kawai, don haka mukan tabbatar an biya mu tarar a safiyar Litinin.”