Mai shanyewar barin jiki ya mutu a gidan mata

Magidancin ya yi tafiyayya daga wata jiha zuwa wajen farkarsa, inda a nan mutuwa ta dauke shi

Mai shanyewar barin jiki ya mutu a gidan mata

Gawa

Wani magidanci da ake zato ya yi tafiyayya zuwa wurin farkarsa tun daga Jihar Delta zuwa ya gamu da ajalinsa a dakinta a Jihar Bayelsa.

Kamar yadda muka samu labari, shi dai wannan mamaci da ya yi tafiyayya me tun daga jihar Delta zuwa wurin farkar tasa, yana fama da larurar shanyewa barin jiki.

Haka kuma majiyar labarinmu ta tabbatar cewa magidancin, mai kimanin shekara 40 a duniya yana da ’ya’ya 12 da ya baro ya je Bayelsa wurin farkar tasa.

Duk kokarin da jama’a suka yi na gano dangi ko ’yan uwansa ya ci tura, karshe dai sai hukumar tsaro aka sanarma wa.

Ya zuwa rubuta wannan labari babu wani dan uwa ko dangin mamacin da ya rasa ransa a dakin farkarsa ranar Talata daga gabata.

Lamarin dai ya jefa mata masu zaman kansu a gidajen da ke unguwar cikin zullumi da firgici har ta kai su ga kwashen komatsensu suna boyewa saboda ba su da tabbas akan aikin da hukuma zata yi idan har aka zo binciken.

Kwamandan ’yan sintiri (VGN) a Jihar Bayelsa, Tolumobofa Akpoebibo Jonathan, ya shaida wa wakilinmu cewa mamacin mai limamin shekara 40 da haihuwa nada yaya 12, kuma ya zo Yenagoa me takanas daga jihar Delta wurin farkar tasa.

Majiyar Yan sanda ta tabbatarwa Wakikinmu mutuwar mutumin, wanda aka sakaya sunansa.

ASP musa Mohammed, kakakin rundunar ’yan sandan jihar Bayelsa, ya shaida wa Aminiya cewa suna kan bincike domin gano ainihin sanadiyar mutuwar mutumin, wanda ake zato cutar shanyewar baryar jiki ce ta yi sanadin mutuwarsa a dakin farkar tasa.