Mai shari’a Saddiq Mahuta ne sabon Galadiman Katsina
Aranar Talata ce Masasautar Katsina ta bayyana tsohon Babban Jojin Jihar Katsina, Mai shari’a Saddik Abdullahi Mahuta a matsayin sabon Galadiman Katsina Hakimin Malumfashi na 11. Hakan ya biyo bayan rasuwar Galadima na 10, Mai shari’a Mamman Nasir a kwanakin baya. Wata takarda da Masarautar Katsina ta aika wa sabon Galadiman a ranar Talata dauke […]
Aranar Talata ce Masasautar Katsina ta bayyana tsohon Babban Jojin Jihar Katsina, Mai shari’a Saddik Abdullahi Mahuta a matsayin sabon Galadiman Katsina Hakimin Malumfashi na 11. Hakan ya biyo bayan rasuwar Galadima na 10, Mai shari’a Mamman Nasir a kwanakin baya.
Wata takarda da Masarautar Katsina ta aika wa sabon Galadiman a ranar Talata dauke da sa hannun Mai martaba Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir Usman, Sarkin ya tabbatar masa da cewa shi aka zaba a matsayin Galadima.
“A bisa kaddarawar Ubangiji, a yau Mai martaba Sarkin Katsina ya tabbatar da bayar da sarautar Galadiman Katsina Hakimin Malumfashi ga Mai shari’a Saddik Abdullahi Mahuta (mai ritaya). Sabon Galadiman shi ne tsohon Babban Jojin Jihar Katsina kuma dan marigayi tsohon Galadiman Katsina Abdullahi Mahuta. A madadin masoyan Mai martaba Sarkin Katsina, muna taya shi murna da sauran jama’arsa na Gundumar Malumfashi,” inji takardar Mai lambaKEC/004 MLFLG/Bol.II/159.
An haifi Galadima Saddik Abdullahi Mahuta a garin Katsina, a ranar 24 ga watan Mayun 1949. Ya fara makaranta a garin Mahuta a 1966, inda daga nan ya ci gaba da neman ilimi a Hadeja da ke Jihar Jigawa a yanzu da Malumfashi, inda ya kammala makarantar babbar firamare. Ya kammala karatun gaba da firamare a Sakandaren Gwamnati ta Funtuwa a 1967. Ya yi karatun share fagen shiga jami’a a Kwalejin Abdullahi Bayero, inda daga bisani ya yi karatun Shari’a a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, daga bisani kuma ya wuce Makarantar Shari’a da ke Legas, wacce ta ba shi damar zama kwararren lauya. Ya yi hidimar kasa a garin Minna, Jihar Neja.
Galadima Saddik Mahuta, wanda mutum ne mai kwarjini da taimakon al’umma, ya yi Babban Jojin Jihar Katsina na tsawon shekara 22. Ya yi ritaya a ranar Juma’a, 24 ga Mayun shekarar 2013.
Nan gaba ne Masarautar Katsina za ta sanar da rana da lokacin da za a yi masa nadin sarautar.