Mai shayi ya kashe saurayi saboda taliyar yara a Jigawa

Mai shagon ya zargi saurayin da sace masa kayan shayi a garin Jigawar Tsada da ke Karamar Hukumar Duse a Jihar Jigawa.

Mai shayi ya kashe saurayi saboda taliyar yara a Jigawa

Wani mai sana’ar sayar da shayi ya lakada wa wani saurayi duka har sai da rai ya yi halinsa saboda taliyar yara a Jihar Jigawa.

Wannan mummuan lamari ya faru ne bayan mai shayin dan shekaru 40 ya zargi saurayin mai shekaru 20 da sace masa kayan shayi, a garin Jigawar Tsada da ke Karamar Hukumar Duse a Jihar Jigawa.

Mai shayin ya zargi mamacin da satar taliyar yara da burodi da madara da kuma man fetur a shagon, lamarin da ya kai ga sa-in-sa a tsakaninsu.

Ana cikin haka ne mai shayin, a fusace ya daure saurayin da igiya, ya yi masa bulala har ya kai ga daina mostsinsa.

Daga bisani ’yan sanda suka je suka kwace shi suka garzaya zuwa asibitin koyarwa na Rasheed Shekoni, amma da zuwansu aka tabbatar da mutuwarsa.

Sanarwar faruwar lamarin da kakakin rundunar ’an sanda da Jihar Jigawa, DSP Lawan Shiisu Adam, ya sanyawa hannu a ranar Talata ta ce, wanda ake zargin ya amince da aikata laifin, inda ya bayyana cewa yawan satar da mamacin ke masa ne ta fusata shi.

A cewasa, wanda ake zargin ya shaida wa masu bincike cewa a baya ya sanar da iyayen mamacin, amma babu wani mataki da aka dauka.

Jimi’in ya ce, makwabta sun ce sun ji kukan mamcin na neman agaji amma sun kasa shiga tsakani har sai da ’yan sanda suka iso.

Daga nan sai ya ce bayan  cikakken bincike za a gurfanar da wanda ake zargi da kisan a gaban kotu domin ya fuskanci hukunci.

Gwamnatin Kano na shirin tara harajin 80bn a 2025

Kirsimeti: Zulum ya ɗauki nauyin jigilar fasinjoji 710 zuwa garuruwansu

Ɗan shekara 60 ya rasu a hatsarin kwalekwale a Sakkwato

Yadda gobara ta ƙone kasuwar babura a Zamfara