Mai shekara 103 ta ƙi aure tana jiran saurayinta
Wata rana John ya samu kira na gaggawa kan ya koma garinsu, ya tafi bai yi bankwana ba, sai na ji baƙin ciki ya kama ni.
Wata mata mai suna Mariam, mai shekara 103, ta bayyana labarin soyayyarta, mai ratsa zuciya da kuma hakurin da ta yi, inda ta bayyana yadda take jira duk ta sadaukar da rayuwarta ga mutumin da bai dawo ba.
Budurwa Mariam ta ba da labarin yadda take ji game da jiran John, matashi mai yawon buɗe ido wanda yake Bature ne da ta haɗu da shi a lokacin ƙuruciyarta.
John, wanda ya yi tafiya zuwa kasar Tanzaniya domin yawon buɗe ido, ya kulla alaƙa ta kud da kud da Mariam, wadda ta taimaka masa wajen samun sabon muhallinsa lokacin da suka haɗu, inda alaƙar soyayya ta ƙullu a tsakaninsu.
“Na haɗu da John, matashi daga Turai wanda ya zo Tanzaniya don neman ilimin yawan buɗe.
“Na taimaka masa ya zagaya garin ya zauna a cikin sabon muhallinsa.
“Bayan wani lokaci, abokantakarmu ta ƙara gaba zuwa wani abu. Ya bambanta da kowa da na taɓa haɗuwa da shi.
“Ɗabi’unsa da labaransa da kyautatawarsa sun burge ni,’’ in ji Mariam.
Dangantakarsu ta ƙara zurfi, kuma Mariam tana matuƙar son John, wanda ta bayyana ta maida hankalinta kansa.
Sun yi musayar mafarki da fatan aure tare. Duk da haka, tafiyar John ba zato ba tsammani ya rusa mafarkin Mariam.
“Wata rana John ya samu kira na gaggawa kan ya koma garinsu, ya tafi bai yi bankwana ba, sai na ji baƙin ciki ya kama ni, na yi ta neman sa tsawon shekaru, ina mai fatan zai dawo,” in ji ta.
Duk da shuɗewar lokaci, Mariam ta ci gaba da jajircewarta ga al’adunta, tana kiyaye budurcinta da fatan auren John.
Ta yi imanin kiyaye budurcinta har zuwa aure wanda ya samu gindin zama a cikin al’adarta.
“Na kasance budurwa, kamar yadda ake sa rai a al’adarmu don kiyaye tsaftar jiki har zuwa aure.
“Kodayake ina kaunar John sosai kuma muna da dangantaka mai ban mamaki, na dage wajen kiyaye wannan al’ada,” in ji Mariam.
Duk da haka, ta ci gaba da yin ƙudiri a kan alƙawarin da ta yi wa kanta da kuma imaninta na al’ada.
“Na ki yarda cewa watakila ba zai dawo ba, duk da abubuwan ban mamaki da muka yi.
“Na yi imanin cewa John zai dawo daga watarana,” in ji ta.
Matar mai shekara 103 ta jaddada cewa tana da yakinin cewa wata rana za ta auri John kuma haƙurin da ta yi za ta samu lada.
“A yayin da shekaru ke tafiya fatan dawowarsa ya fara dusashewa ya bar ni da kin cin amana kuma ni kaɗai, duk da haka, na ci gaba da kulla alkawari da kaina da al’ada ta,” in ji ta.