Mai shekara 103 ya auri ’yar shekara 27 a Indonesiya
Tun a watan jiya ne kafafen sada zumunta a kasar Indonesiya suka shiga tafka muhawara a kan wani aure da aka yi mai sarkakiya a Kudancin garin Sulawesi, inda wani dan kasar Holland mai shekara 103 ya auri wata mata ’yar shekara 27. Hotuna da bidiyon ma’auratan sun dauki tsawon mako daya suna yawo a […]
Tun a watan jiya ne kafafen sada zumunta a kasar Indonesiya suka shiga tafka muhawara a kan wani aure da aka yi mai sarkakiya a Kudancin garin Sulawesi, inda wani dan kasar Holland mai shekara 103 ya auri wata mata ’yar shekara 27.
Hotuna da bidiyon ma’auratan sun dauki tsawon mako daya suna yawo a kafafen sada zumuntar inda suka janyo hankalin jama’a suke tofa albarkacin bakunansu. Akwai dai wadanda suke tunanin labarin ba gaskiya ba ne, amma manyan kafafen watsa labarai na kasar Indonesiya sun tabbatar da faruwar lamarin. Mutumin mai suna Puang Katte, wanda ya auri matar mai suna Indo Alang, yana daya daga cikin wadanda suka taka rawa a yakin neman ’yancin kasar Holland daga 1945 zuwa 1949.
Jaridar Tribune News, ta ce shekarun mutumin sun kai 103 inda matar take da shekara 27, wato akwai bambancin shekara 76 a tsakaninsu, wanda hakan ya sa wadansu mazauna yankin cika da mamakin aure a tsakanin ma’auratan biyu. A shekarar 2017 ma an ruwaito wani rahoto inda wata mata mai shekara 71 ta auri wani matashi mai shekara 16, a kasar.
Hotunan bidiyon sun nuna yadda matar take dafa wa angon nata abinci yayin da ya taho ya samu amaryar tasa. Hakan ya sanya shakku ko auren soyayya ne ko kuma shiryayyen al’amari.
Abin al’ajabi game da auren na bayan nan shi ne sadakin da mutumin ya biya. Kafafan labarai a yankin Sulawesi sun ce ya biya Dalar Amurka 343 da kuma zoben zinare. A halin yanzu ma’auratan suna rayuwa ne a gidansu da ke Kudancin garin Sulawesi.