Mai shekara 23 ya angwance da ’yar shekara 45
Matashin ya angwance da mai shekara 45 wadda ’yar siyasa ce.
Wani matashi mai shekara 23, ya angwance da wata mai shekara 45 a Jihar Adamawa.
A kwanan baya ne labari da hotunan auren suka karade shafukan sada zumunta a Najeriya, kamar yadda kafar labarai ta VoA Hausa ta ruwaito.
An wallafa hotunan sabbin ma’auratan a shafukan Twitter da Instagram, hade kuma da katunan bikin auren nasu.
Koda yake kafar labaran ta ce babu cikakken bayani game da angon da aka bayyana cewa sunansa Adam Dalla, amaryar tasa mai suna Barista Jamila Babuba kuma sananniyar ’yar siyasa ce kuma ’yar fafutuka a jihar ta Adamawa.
Rahotanni sun ce, Honarabul Jamila Babuba, kamar yadda wasu suka fi sanin ta, ta taba yunkurin tsayawa takarar kujerar Majalisar Wakilai ta ta Yola ta Kudu da ta Arewa da Girei a Jihar.
Bayanai sun ce an daura auren ne a ranar 18 ga watan Mayu, 2021, za kuma a yi shagalin bikin auren a ranar Lahadi 31 ga watan.
Auren ya ja hankali inda galibi mutane suke jinjina wa ma’auratan, tare da yi musu fatan alheri.
Haka kuma auren na Dalla da Jamila, ya kara jaddada sabuwar kalmar Hausa ta ‘wuf’ da ake amfani ita domin bayyana irin wannan al’amari.
Ko bayan tsokacin da jama’a ke yi dandalin sada zumunta, a daya gefen murna ce ta karade birnin Yola sakamakon bikin auren.