Mai shekara 60 ya shiga hannu bayan ya sace wayoyin Android 70
An gano wayoyi masu tarin yawa da kwamfutoci da sauran kayan sata a gidansa.
Dubun wani mutum mai shekara 60 ta cika inda aka kama shi da wayoyin sata guda 70 kirar Android da kwamfutocin Laptop da sauran abubuwa.
Jami’an hukumar tsaro ta NSCDC sun kama mutumin ne bisa zargin hada baki wajen fasa gidajen mutane da kuma aikata sata a Jihar Kwara.
- Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da shirin ‘N-Knowledge’
- Maciji ya sare shi a hanya bayan ya gudo daga hannun masu garkuwa da shi
Hukumar ta ce tsohon mai suna Bolaji shi ne mai ajiyar kayan da abokin hadin bakin nasa mai suna Shittu — wanda ya kware wajen fasa gidaje ya shiga ya yi sata — yake sato musu.
Mai magana da yawun hukumar NSCDC a Jihar Kwara, Babawale Zaid Afolabi, ya ce dubun tsohon ta cika ne bayan an kama Shittu, wanda shi kuma a wurin bincike ya fallasa alakar da ke tsakaninsu da kuma inda ake ajiyar kayan satan.
Jami’in ya ce hukumar ta kama Shittu ne bayan wata mai suna Yemisi Adefila da ke zaune a unguwar Oko Oba da ke yankin Gaa Akanbi ta kai kara cewa ya fasa gidan iyayenta ya shiga, ya sace musu kayayyaki.
Babawale ya shaida wa Aminiya cewa baya ga wayoyi kirar Android guda 70 da kwamfutocin da aka kama a gidan Bolaji, sauran abubuwan da aka gano sun hada da kayan kallo da sauran abubuwa da aka tattara aka tafi da su domin gudanar da bincike a ofishin hukumar.