Mai shekara 70 ta haifi danta na farko
Ta haifi danta na farko ta hanyar dashen maniyi.
Wata mata a kasar Indiya za ta iya shiga kundin tarihi na duniya a matsayin daya daga cikin tsofaffin mutanen da suka taba haihuwa suna masu yawan shekaru.
Tsohuwar mai suna Jivunben Rabari, wacce ake kyautata zaton tana da shekara 70 a duniya, ta ce ta haifi danta na farko ta hanyar dashen maniyi (IVF).
- An fara sayar da babur mai tashi sama
- Ya sayar da kodarsa ya sayi wayar iPhone, daya kodar kuma ta daina aiki
Jaririn shi ne na farko ga Jivunben da mijinta mai suna Maldhari mai shekara 75, bayan kusan shekara 20 da aurensu.
Sabuwar mahaifiyar, wacce ta fito daga wani karamin kauye da ake kira Mora, a Gujurat, ta ce ba ta da wata takardar shaida don tabbatar da shekarunta, amma ta yi ikirarin ta kai shekara 70.
Wannan zai sa ta zama daya daga cikin tsofaffin uwaye na farko a duniya.
Likitan da ya taimaki ma’auratan don samun dan mai suna Dokta Naresh Bhanushali, ta hanyar IVF, ya ce: ‘Lokacin da suka fara zuwa wurinmu, sun fada mana cewa ba za su iya haihuwa ba a irin wannan tsufan nasu, amma sun dage kan neman haihuwa.
“Sun ce da yawa daga cikin danginsu ma sun yi irin hakan don samun da. Wannan yana daga cikin abin al’ajabin da na taba gani,” inji likitan.
Yayin da yawancin juna biyu ke haifar da jariri lafiyayye da damar samun matsaloli na tasowa tare da yanayin yawan shekaru, masanan sun yi gargadi ga mutanen da suka haura shekara 40 cewa suna cikin hadarin rasa samun haihuwa.
A cewar rahoton Kwalejin Kwararrun Likitoci da Masana Kiwon Lafiyar Mata (RCOG), mafi kyan shekarun haihuwa shi ne daga 20 zuwa 35.
Yawancin mutanen da suka haura shekara 45 ba za su iya daukar juna biyu ba, ba tare da taimakon IVF ba, kuma tsofaffi sun fi shan wahala kan hakan.
Kungiyar Likitocin Haihuwa ta Amurka (ASRM) ta ce, mata na kowane zamani za su iya samun juna biyu da taimakon likita, da sharadin suna da ‘lafiyayyar mahaifa’, koda kuwa ba ta da kwai.
Adadin samun nasara daya ne a cikin 50 ga mata sama da 44, balle wadanda ke cikin shekara 70.
Amma a cikin shekarar 2019, kafar yada labarai ta Metro.co.uk ta ba da rahoton yadda wata mace ’yar Indiya, mai suna Erramatti Mangayamma, ta yi maraba da samun tagwaye ta hanyar IVF wacce take da shekara 74.
Wannan ya sa ta zama mace mafi tsufa a duniya da ta haihu a lokacin.
A lokacin da ta wuce shekarun uwa mai haihuwa a duniya, mai suna Daljinder Kaur, daga Punjab, wacce ta haihu tana da shekara 70 a shekara ta 2016.