Mai shekara 73 ta sauke Alkur’ani a Kano
Malamarta, Sayyada Saudatuz-Zam’an ta ce dattijuwa Binta ta kasance mai hazaka
A karshen makon da ya gabarta ne wata dattijuwa mai kimanin shekara 73 mai suna Hajiya Binta Muhammad Bakanbare ta shiga cikin jerin daliban da suka sauke Alkur’ani mai girma a Makarantar Gidan Malam Abdussalam da ke Unguwar ’Yakasai, Kano.
Hajiya Binta ta shaida wa Aminiya cewa tun tana yarinya take shaukin karatun Alkur’ani sai dai ba ta samu damar hakan ba sakamakon aure da aka yi mata da wuri.
- Yadda aka ceto daliban Kankara a Dajin Zamfara
- Yadda muka sansata aka sako Daliban Kankara ba biyan kudin fansa
A cewarta ta dauki tsawon shekara takwas tana bibiyar makarantu inda ta sake bitar karatunta na baya kafin daga bisani ta dora a inda ta tsaya.
“To kasancewar an yi min aure da wuri ina da shekara 13 to hakan ya sa ban samu damar yin karatu mai zurfi ba.
“Sai a yanzu Allah Ya nufe ni da ci gaba. Kuma Allah Ya taimakeni na kammala. Alhamdulillah.”
Sayyada Saudatuz-Zam’an Shaikh Nasir Kabara, ita ce malamar da dattijuwa Binta ta yi sauka a hannunta, ta bayyana ta a matsayin zaliba zakaqura wacce ta kere sa’a a cikin dalibai.
“Gaskiya ta kasance daliba mai hazaka. Tana mayar da hankali sosai a kan karatunta musamman abin da ya shafi Alkur’ani da dala’ilu.”