Mai shekara 82 ta yi gudun mil 78 a cikin sa’o’i 24
Babu maganin da nake na sha, baiwar kuzari ce kawai.
Wata tsohuwa mai suna Barbara Humbert, mai shekara 82 daga garin Bal d’Oise da ke kasar Faransa, ta kafa sabon tarihi a duniya bayan ta yi gudun kilomita 125 (mil 78) a cikin sa’o’i 24.
A gasar cin kofin Faransa da aka gudanar a Bribe-la-Gaillarde, Barbara Humbert mai shekara 82, ta kafa tarihi a duniya na tsere mafi tsawo a cikin sa’o’i 24 a bangaren masu shekarunta.
- NAJERIYA A YAU: Yadda ’Yan Siyasa Ke Raba Kan ’Yan Najeriya, Su Kuma Kansu A Hade
- ‘Yawan shan kwayar Farasitamol na shafar hanta’
Wata Bajamushiya ce ta yi gudun kilomita 105 (mil 65.2) a kan kwalta a shekarun baya, kuma Barbara na da burin inganta wannan tarihi da kimanin kilomita 15.
Ta zarce abin da ake tsammani, duk da haka, ta shafe wancan tsohon tarihi na duniya da nisan kilomita 125 da aka shafe cikin sa’o’i 24.
Wadansu na tambaya kan ko tsohuwa mai shekara 82 tana iya yin wannan bajintar? Kodayake za a iya rantsewa cewa, tana gudun famfalaki tsawon rayuwarta, Barbara ta fara gudu ne tana da shekara 43, a lokacin da ’yarta ta fara shirin jarrabawar kammala sakandare.
Bayan an koya mata dabarun numfashi mai kyau. Bafaranshiyar ta sa kayan wasanta kuma ta fara gudu a kan titunan Bouffémont (a Bald’Oise) inda take zaune.
Da farko ta fara cikin nishadi ta bi ta titunan garinsu ba da dadewa ba ta koma tsere a birane, sannan ta zama cikakkiyar ’yar tseren famfalaki.
A cikin shekara 39 da ta shafe tana gasar tseren, Barbara Humbert ta halarci gasar tsere 137 da gudun famfalaki 54, ciki har da na Paris da New York. “Ina samun ’yanci lokacin da nake gudu a kan tituna.
“Ina shigar da nau’i na tunani. Na kawar da hankalina,” kamar yadda tsohuwar ta bayyana wa jaridar Ouest France bayan nasarar da ta samu a baya-bayan nan.
Da take magana game da tseren kanta, Humbert ta ce, ba ta jin gajiya ko kadan a cikin sa’o’i 24, ba ta taba jin barci a cikin daren da za ta yi ba, kuma ta tilasta wa kanta ta ci da sha.
Sai dai gajiyar ta shiga cikin jikinta bayan ta tsallake iyakar wasan, kuma ta yi imani cewa wannan na daga cikin dalilan da suka sa aka dauki kwanaki kafin ta fahimci muhimmancin nasarar da ta samu.
Da aka tambaye ta abin da ya ba ta kuzarin da ta kai ga iyakar cin nasarar gasar, Barbara ta ce mijinta ne ya ba ta karfin gwiwa zuwa shiga gasar a duk tsawon tseren na sa’o’i 14, kuma sha’awarta ta sa wasu su yi alfahari, musamman, mambobin kungiyarta ta tsere ta Saint Brice Athlétisme (SBA).
A lokacin tseranta mai ban sha’awa, Barbara Humbert ta samu raunuka da dama, ciki har da ciwon cinya da ciwon idon kafa da jijiyoyin kafa, amma ba ta bar wadannan matsalolin su ci karo da abin da ta fi so ba.
“Ba na shan magani, kuma na ci gaba da samun horo,” inji matar mai shekara 82.
“Kada ku daina gudu na dogon lokaci idan ba haka ba za ku ji kunya a wasan tsere,” inji ta.