Mai shekara 98 din da ta shiga firamare na son zama likita a nan gaba
Tsohuwar ta ce ba ta da burin da ya wuce ba zama likita a nan gaba
A cikin wani dakin karatu da aka gina da dutse a karkarar tsaunin Rift Valley na Kenya, wata tsohuwa mai suna Priscilla Sitienei, wacce ta cika shekara 98 a ranar Juma’ar makon jiya, aka hango tana yin rubutu tare da daliban ajinta wasanda dukkansu ta girme su da sama da shekara 80.
Tana sanye da kayan makaranta masu launin toka da koriyar suwaita, Priscilla ta ce, ta shiga makarantar ce domin ta
zama misali mai kyau ga jikokinta da kuma koyon sabuwar sana’ar da za ta kware a gaba.
- Mutum 12 sun mutu a hatsarin mota a Kwara
- Saboda zaben 2023 muka dakatar da cire tallafin mai – Minista
“Zan so zama likita saboda in kasance ungozoma,” ta shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters, inda ta qara da cewa, ’ya’yanta suna goyon bayan shawarar da ta yanke.
A shekarar 2003 ne Gwamnatin Kenya da ke gabashin Afirka ta fara bayar da tallafin kusin shiga makarantun firamare, wanda hakan ya bai wa wadansu tsofaffi da suka kasa samun ilimi a lokacin da suke yara su farfado da burinsu.
Wannan ya sa wadansu tsofaffin daliban da suka nuna kwazo a baya, ciki har da Priscilla, wadda ta je birnin Paris a bara
domin kaddamar da wani fim kan ziyarar da ta kai mai suna ‘Gogo’ da ke nufin kaka ta uwa a harshen Kalenji.
Haka nan ba da jimawa ba za ta nufi birnin New York domin jaddamar da wani fim din.
Priscilla, wacce ke aji na shida a firamaren ta ce, mafi girman burinta ya fi zama jarumar fina-finai.
Ta ce, tana da ra’ayin hakan ne lokacin da jikarta ta bar makaranta bayan ta samu juna biyu.
“A cikin zolaya da aka tambaye ta, ko akwai sauran kudin da ya rage mata a makaranta sai ta ce, eh haka ne akwai, na gaya mata cewa zan yi amfani da shi don fara makaranta.”
Ta yi fatar jikarta za ta koma karatu, inji ta, amma da ta ki, sai Priscilla ta yanke shawarar komawa makarantar da kanta.
Ta ce, tana jin dadin sauran harkokin makarantar tare da sauran jikokinta, gami da karatun motsa jiki.
“Yana iara min lafiya. Ina yin tsalle-tsalle, kodayake ba kamar yadda sauran daliban za su yi ba, amma akalla ina motsa jikina. Abin farin cikina ke nan,” inji ta.
Malamanta suna gwada kwarewarta don samun zaman lafiya yayin darussa.
A cewar malamin Priscilla, “Na sa ta zama mai kula da aji tana neman masu surutu a cikin aji. Don haka, ta samu damar yin wannan aiki. Idan na fita waje, ajin yana yin shiru,” inji malamin mai