Mai sunan da ke dauke da haruffa 36 ta samu lasisin tukin mota

Wata mata a Amurka, ’yar asalin tsibirin Hawaii, mai suna da ke dauke da haruffa 36, ta samu lasisin tukin mota, bayn an sha daga wajen samar da katin da zai rika daukar sunaye masu tsawo. Matar mai suna Janice “Lokelani”  Keihanaikukauakahihuliheekahaunaele, ta ce tana cike da farin ciki, da nasarar da ta samu wajen […]

Mai sunan da ke dauke da haruffa 36 ta samu lasisin tukin mota

Mai suna da haruffa 36 ta samu lasisin tukiWata mata a Amurka, ’yar asalin tsibirin Hawaii, mai suna da ke dauke da haruffa 36, ta samu lasisin tukin mota, bayn an sha daga wajen samar da katin da zai rika daukar sunaye masu tsawo. Matar mai suna Janice “Lokelani”  Keihanaikukauakahihuliheekahaunaele, ta ce tana cike da farin ciki, da nasarar da ta samu wajen fafutikar ganin an warware matsalar tsawon sunanta, inda aka samar da katin da zai dauki sunaye masu tsawo irin nata.
Lasisin tukin mota da katin dan kasa, a da ba su da isasshen filin rubuta sunayen da yawan harufansu suka kai 35, sai ga shi sunanta yana dauke da haruffa 35, tare da wata alama da a tsaribn rubutun haruffan Hawaii ake yi wa lakabi da ‘okina.
Sabon tsarin bayar da katin, ya fito da isasshen filin rubuta sunayen da yawan haruffansu ya kai 40, ga sunan farko, tare da haruffa 35 ga sunan tsakiya.

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda

‘Yan bindiga sun ƙone gidan mai da motoci 4 a Enugu

Kwalara ta kashe fiye da mutum 300 a Sudan