Mai taimaka wa Gwamna ya ba ’yan bumburutu tallafi
Mai taimaka wa Gwamnan Jihar Gombe kan ayyuka na musammam Alhaji Abubakar Manzo Sarkin Doya, ya gana da ’yan kasuwar man fetur ta bayan fage da ke jihar don fadakar da su game da sake zaben Gwamna Ibrahim dankwambo karo na biyu a bana. Alhaji Abubakar Manzo Sarkin Doya, ya gana da ’yan kasuwar ne […]
Mai taimaka wa Gwamnan Jihar Gombe kan ayyuka na musammam Alhaji Abubakar Manzo Sarkin Doya, ya gana da ’yan kasuwar man fetur ta bayan fage da ke jihar don fadakar da su game da sake zaben Gwamna Ibrahim dankwambo karo na biyu a bana.
Alhaji Abubakar Manzo Sarkin Doya, ya gana da ’yan kasuwar ne a dakin taro na Ma’aikatar Harkokin Mata inda ’yan kasuwar da dama suka halarta, kuma ya shaida musu nasarorin da Gwamnan ya cimma a bangarori daban-daban.
Abubakar Sarkin Doya, ya yi kira ga ’yan kasuwar su ba Gwamna dankwambo kuri’unsu don ganin ya zarce a zaben da ke tafe domin ci gaba da tsare-tsarensa na kawo ci gaba a jihar.
Ya bada sanarwar bai wa kowane dan kasuwar bumburutu da ya halarci taron tallafin Naira dubu goma don kara jari a harkar kasuwancinsa.
Malam Shehu Manzo ya ce taron wani bangare ne da mai taimaka wa Gwamnan ya yi don ganin an sake zabensa a karo na biyu.
A jawaban Baffalo Ahmad da Abdul Mega da Bala Wandaful, jinjina suka yi ga mai taimaka wa Gwamnan, dangane da kokarinsa, kuma sun yi kira ga ’yan siyasa su yi koyi da shi, inda suka yi alkawarin ci gaba da bada goyon bayansu ga Gwamna dankwambo a zaben na bana.