Mai tattaki don Buhari: Ban zama miloniya ba
Matashin nan Sulaiman Hashimu da ya yi doguwar tafiya a kasa daga Legas zuwa Abuja domin murnar nasarar da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi a zaben kwanan baya, ya nuna rashin jin dadinsa da irin labaran karya da jita-jitar da wasu ke bazawa cewa ya sami makudan kudade.Ya ce wannan jita-jitar a halin yanzu ta […]
Matashin nan Sulaiman Hashimu da ya yi doguwar tafiya a kasa daga Legas zuwa Abuja domin murnar nasarar da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi a zaben kwanan baya, ya nuna rashin jin dadinsa da irin labaran karya da jita-jitar da wasu ke bazawa cewa ya sami makudan kudade.
Ya ce wannan jita-jitar a halin yanzu ta haifar da barazana ga rayuwarsa da tabarbarewar dangantaka a tsakaninsa da wasu ’yan uwansa da abokan arziki.
“Tun daga ranar da aka yi mani iso ga Shugaba Muhammadu Buhari, muka gaisa hannu da hannu kuma ya jinjina mani a kan bajintar da na yi sai kawai wasu mutane suka rika bayar da labaran karya cewa, wai na zama miloniya daga irin dimbin kudade da motoci masu tsada da na samu daga hannun sarakuna da gwamnoni da manyan ’yan siyasa. Wannan jita jitar ta haifar da tabarbarewar zumunci a tsakanina da wasu ’yan uwana da abokan arziki da wasu suke tunanin na samu na guje su.”
Da yake karyata jita-jitar cikin tattaunawa da wakilinmu ta wayar tarho, Sulaiman ya yi rantsuwa kamar haka: “Wallahi Tallahi babu kamshin gaskiya a cikin wannan al’amari. Ni dai na yi wannan tafiya ne saboda kaunar Shugaba Buhari amma ba domin samun wani abu ko neman wata alfarma ba. Wani Sanata da Wakilin Majalisar Tarayya (an boye sunayensu) su ne kadai suka ba ni kyautar Naira dubu 50 da Naira dubu 30 a jere domin nuna farin cikinsu da irin abun da na yi. Kuma sun ba ni ne ba tare da na roke su ba. Motar da nake hawa a yanzu, ni na saye ta da kudin aljihuna. Babu wanda ya taba ba ni mota ko babur. Saboda haka nake kokarin yin tafiya zuwa mahaifata Funtuwa domin yi wa iyaye da ’yan uwa bayanin gaskiyar halin da nake ciki tare da n eman gafararsu.”
Da yake amsa wata tambaya, matashi Sulaiman ya ce: “Yanzu haka da muke tattaunawa da kai a yau talata 21 ga watan Yuli, na kawo ziyarar ban girma da Barka da Sallah ne ga mai martaba Sarkini Bidda da kallon hawan Sallah da ake yi a fadarsa a wannan rana. Kuma har zuwa yau ina rakube ne a cikin gidan wani abokina a Abuja ba cikin otal da aka sauke ni tun farko ba. Sannan kuma, a lokuta daban-daban muna haduwa da uwargidan Shugaba Buhari muna gaisawa da ita da sauran mukarraban shugaban da suke tare da mu a lokacin da aka isar da ni gare shi.”