Mai tuki cikin maye ya zargi karensa kan harigidon mota
An kama wani mutum da laifin tuki a cikin maye a Jihar Florida ta kasar Amurka, inda shi kuma ya dora alhakin harigidon da motarsa ke a yi a kan tukin karensa.Jami’an ’yan sandan garin Manatee sun tsyar da farar mota mai kofa hudu da ke gudu da harigido a kan titukin karensa ne ya […]
An kama wani mutum da laifin tuki a cikin maye a Jihar Florida ta kasar Amurka, inda shi kuma ya dora alhakin harigidon da motarsa ke a yi a kan tukin karensa.
Jami’an ’yan sandan garin Manatee sun tsyar da farar mota mai kofa hudu da ke gudu da harigido a kan titukin karensa ne ya haifar da matsalar.
Da wannan direba ya yi kokarin gyara tafiyar motar, sai kawai ya bi ta kan wani rami da ke gefen hanyar dab a hannun tukinsa ba.
Mutumin da ake tuhuma da aikata wannan laifi, mai suna Reliford Cooper, ya yi kokarin tserewa da kafa, ammam sai jami’an tsaron K9 suka tsinci rigar singiletinsa a kofar coci.
Faston Cocin ya bayyana wa mataimakins acewa, wani ya buya a cikin bandakin cocin. Sai kuwa mahalartan cocin suka tursasa Cooper da karfi har ya fito, har aka kama shi.
Da aka sanya masa ankwa, sao Cooper ya rika cewa: “ba ni ke tuki ba. Wane ne ke bi na? Kun yi sanyin jiki (ya furta da karfi)!
daya daga cikin jami’an tsaron ya sanar da Cooper cewa yana warin barasa da wiwi, al’amarin day a sanya ya bayar da bayanai barkatai.
“Karena ke tukin. Na gudu ne don ina son yin hakan. Ba za ku samu kwayoyi ko bindiga a jikina ba,” a cewar Cooper, inda daga bisani ya yi amai, ya kuma koka da ciwon baya.
Ana tuhumar Cooper da laifuffukan da suka hada da tuki cikin maye da bata gidan wasu, da kokarin gudu daga hannun hukuma. Yanzu an tafi da Cooper zuwa asibiti don binciken laifiyarsa, inda daga bisani za a wuce da shi kurkuku.