Mai unguwa ya gane wanda ya yi garkuwa da shi

A karshen mako jiya ne Rundunar ’Yan sandan Jihar Nasarawa ta gabatar da wadansu matasa biyar da ake zargi da yin garkuwa da Mai unguwar kauyen Hunki da ke Karamar Hukumar Awe Alhaji Umaru Jibrin ga manema labarai. Lokacin da Kwamishinan ’Yan Sandan  Jihar Mista Bola Longe ke gabatar da wadanda ake zargin ga manema labarai […]

Mai unguwa ya gane wanda ya yi garkuwa da shi

Alhaji Umaru Jibrin

A karshen mako jiya ne Rundunar ’Yan sandan Jihar Nasarawa ta gabatar da wadansu matasa biyar da ake zargi da yin garkuwa da Mai unguwar kauyen Hunki da ke Karamar Hukumar Awe Alhaji Umaru Jibrin ga manema labarai.

Lokacin da Kwamishinan ’Yan Sandan  Jihar Mista Bola Longe ke gabatar da wadanda ake zargin ga manema labarai ya bayyana sunayen wadanda ake zargin da Musa Adamu mai shekara 26 da Umaru Mohammed mai shekara 28 da Nuhu Mohammed mai shekara 38 da Hassan Zakari mai shekara 20.

A cewarsa, jami’ansa ne suka yi nasarar kama mutum hudu daga cikin wadanda ake zargin bayan sun samu bayyanan sirri kan inda suke boye a wani daji a Karamar Hukumar Awe, sannan daga bisani wanda aka sacen wato Mai unguwar Hunki Alhaji Umaru Jibrin da kansa ya kama mutum na biyar daga cikinsu.

Kwamishinan ya ce an gano makamai da layu da wayoyin salula da yawa da kudi sama da Naira dubu 400. Kuma a cewarsa da da zarar an kammala bincike za a gurfanar da su a gaban kotu don su fuskanci hukunci.

Da yake bayyana wa wakilinmu yadda ya shiga tasku a hannun wadanda suka yi garkuwa da shi, Mai unguwar ya ce ya yi kwana biyu ba ci ba sha a hannunsu a cikin daji, inda ya ce sun sace shi ne a gidansa da daddare misalin karfe 3 a ranar 23 ga Yulin da ya gabata. Ya ce daga nan suka kai shi wani daji kafin suka sake shi bayan an biya kudin fansa na Naira dubu 600. “Kasancewa ba ni da hakkinsu bayan sun karbi kudin sun sake ni ne na dawo gida ina jin yunwa kuma ba abinci a gida a lokacin, sai na ce bari in je wani shagon abinci a cikin garin Awe. Bayan na shiga shagon sai na ga daya daga cikin wadanda suka yi garkuwa da ni shi ma ya zo shagon don cin abinci, nan take na fara ihu ina ga wanda ya yi garkuwa da ni. Hakan ya jawo hankalin mutane aka zo aka kama shi aka kai shi ofishin ’yan sanda da ke kusa da shagon abincin,” inji Mai unguwar.

Daya daga cikin wadanda suka yi garkuwa da Mai unguwar wanda aka kama a shagon abincin, Umaru Mohammed ya amince da zargin da ake yi masa, inda ya bayyana cewa abokansa ne suka ja ra’ayinsa wajen aikata laifin. Kuma a cewarsa dukkansu suna zaune ne a garin Awe.