Mai Wandon karfe: Shugaban kasa Janar Muhammadu Buhari
Yau shekara daya ke nan cur da ni GIZAGO (08065576011) na yi wannan tsokacin, wanda na yi shi jim kadan da bayyana sakamakon zaben Shugaban kasa da aka gudanar a baran, inda kuma Muhammadu Buhari ya yi nasara. Muhimman al’amuran da na tattauna a tsokacin, su suka sanya na dawo da shi a yau, da […]
Yau shekara daya ke nan cur da ni GIZAGO (08065576011) na yi wannan tsokacin, wanda na yi shi jim kadan da bayyana sakamakon zaben Shugaban kasa da aka gudanar a baran, inda kuma Muhammadu Buhari ya yi nasara. Muhimman al’amuran da na tattauna a tsokacin, su suka sanya na dawo da shi a yau, da nufin mu sake nazartarsa, mu kuma duba yadda al’amura suke a yau. In Allah Ya yarda za mu dawo mu ga sakamakon da aka samu a wannan mulki, bayan cikarsa shekara daya daidai. A sha karatu lafiya:
Janar Muhammadu Buhari! Wannan sunan ba bako ba ne a kunnuwan al’ummar Najeriya musamman, da na Afirika da ma duniya ba ki daya. Ma’anar sunan na tattare da kalmomin jajircewa, gaskiya, adalci da jarumtaka. Haka kuma, sunan dai yana nuni da rikon amana, tausayin talakawa da sanin ya kamata.
Tun daga makon nan, bayan bayyana sakamakon zaben shugabancin kasa da aka gabatar, sunan nan ya sake daukar sabuwar ma’ana, domin kuwa al’ummar Najeriya sun amince, sun kafe, sun dauki dukkan amanarsu sun damka masa. Ma’ana sun yarda cewa shi ne shugabansu, majagoransu ga dukkan al’amuransu.
Abubuwa da yawa suka sanya al’ummar Najeriya suka amince da shi, har suka yarda da mika masa amanarsu. Wasu daga cikin irin wadannan dalilai su ne, shi dai ya kasance tamkar ta maso salon maganar nan – ‘Mai Wandon karfe.’ Wannan na nufin cewa mutum ne shi jajirtacce, marar kasala, wanda ba ya gajiyawa wajen aiwatar da duk abin da ke gabansa. Mutum irinsa ne ba zai gajiya ba wajen tunkarar aikin gina al’ummarsa.
Mutum ne mai gaskiya, kamar yadda kowa ya yarda kuma ya amince da haka. An jaraba shi a baya kuma ta tabbata bai ci amanar duk wata amana da aka damka masa ba. Ya rike mukamai masu yawa, amma ba a samu inda aka ce an kama shi da almundahana ko satar dukiyar al’umma ba. Ya yi Gwamnan Jihar Arewa Maso Gabas (jihohin Borno, Adamawa, Yobe, Bauchi da Gombe a yanzu). Ya taba rike mukamin Ministan Albarkatun Man Fetur na Najeriya, tun zamanin da fetur ma na fetur dinsa. Ya taba zama Shugaban kasa na mulkin soja. Ya taba rike mukamin Shugaban Asusun Rarar Mai (PTF), inda ya ririta abin da aka ba shi, ya yi ayyukan kirki a dukkan fadin kasar nan.
Dukkan wadannan mukamai da ya rike, bai yi amfani da su ya azurta kansa ba. Ba ya da asusun ajiya a kasar waje, ba ya da wani hamshakin gida a Abuja ko a Dubai, ba ya da wasu kazaman kudi, kamar yadda wasu ’yan siyasa suke da su. Hatta fansho da ake biyan tsofaffin shugabannin kasa na Naira Miliyan 23, shi cewa ya yi sun yi masa yawa, a maimakon haka, ya ce a rika ba shi kashi goma cikin dari na wannan adadi. Don haka ne ake biyansa Naira miliyan biyu da rabi duk wata. Sauran rarar kuma yana mayarwa asusun gwamnatin kasar nan. Wannan ke nuna maka cewa abin duniya bai dame shi ba, kuma haka ke nuna wa al’umma irin gaskiyarsa da iya rikon amana.
A yanzu da Allah Ya damka masa mulkin Najeriya, lallai zama bai same shi ba, domin kuwa akwai kalubale masu yawa da zai fuskanta, kasancewar al’amura da dama sun canza a kasar nan.
Ba kamar lokacin da ya yi mulki a matsayinsa na soja ba, yanzu lokaci ne na dimokuradiyya, inda ’yan majalisa ke da hakki wajen bin kadin yadda mulki ke gudana, kamar kuma yadda bangaren shari’a ke da ta cewa a kowane fanni, kamar kuma yadda kundin tsarin mulki ke zama kankat wajen tafiyar da al’amura, wanda ya sha bamban da dokokin soja. Don haka lallai wannan babban kalubale ne ga Janar Buhari, amma da ikon Allah saboda kyakkyawar niyyarsa, zai samu nasara ta kowane janibi.
Wani abin da zai kawo masa kalubale kuma shi ne, yanayin da Najeriya take a halin yanzu. A halin yanzu, abin da kasar nan ke tinkaho da shi a matsayin dukiyar kasa, wato danyen man fetur, kadarinsa da kimarsa ta karye a duniya. A yanzu ana sayar da ganga guda a farashin kasa da Dala sittin, kuma akwai masu hasashen da ke cewa farashinsa zai ci gaba da karyewa, ta yadda zuwa watan jibi, farshinsa na iya saukowa zuwa Dala 35. Ke nan, madamar Gwamnatin Janar na bukatar ci gaba, dole ta samo hanyoyin samun kudin shiga baicin man fetur.
Game da wannan kalubalen ma, sai mu gode Allah, kasancewar Janar ya yi alkawarin mayar da hankali ga harkokin noma da hako ma’adinai, domin ganin an bunkasa tattalin arzikin kasa da kuma samar wa da al’umma ayyukan yi. Babu shakka, muddin aka jajirce bisa wannan kuduri, da ikon Allah nasara za ta samu, domin kuwa Allah Ya albarkaci kasar nan da albarkar kasar noma, kamar kuma yadda Ya albarkace ta da ma’adinai kala-kala, wadanda duniya ke bukata.
Wani kalubale kuma shi ne, yadda al’ummar kasa musamman ma ma’aikatan gwamnati da mukarrabansu suka lalace, suka zama kuraye, suka zama barayi kamar beraye. Babu abin da ke tashe sai kashe-mu-raba, aringizo da wawashe dukiyar al’umma. Najeriya na bukatar namijin shugaba jarumi, wanda zai taka wa barayi burki, ya dawo da martabar aikin gwamnati.
Nan ma sai mu ce Allah-son-barka, domin kuwa Janar bai da abokin gaba na farko da ya wuce barawo kuma da ikon Allah zai samu nasara ta wannan janibi. Shi dai ba zai sata ba kuma ba zai bari a sata ba, amma zai biya kowa hakkinsa daidai gwargwado.
Wani kalubalen kuma shi ne, zuganyewar tsaro, doka da oda. Al’amuran tsaro sun lalace, jami’an tsaro sun zama masu barazana da ban tsoro. Laifuka sun yi yawa, ta’addaci, satar mutane don garkuwa da su sun yawaita, fashi da makami ya zama ruwan dare.
Wannan ba karamin kalubale ba ne ga Gwamnatin Janar Buhari, don haka akwai bukatar jajircewa domin ganin an dawo wa sojoji da ’yan sanda da sauran jami’an tsaro martabarsu. Hakan kuwa ba abu ne mai sauki ba. Sai dai ganin yadda Janar din ya dauki gammo kuma ya bugi kirjin fuskantar wannan matsala gaba-gadi, daga dukkan alamu zai samu nasara.
Shugaban kasa Janar Muhammadu Buhari, mai jiran gado, ba zai iya samun nasara ba dole sai ya samu hadin gwiwa da goyon bayan al’ummar kasa. Don haka, ina kira ga al’umma cewa: Yadda muka jajirce, muka tsaya kai da fata, muka tsaya cikin dukan rana da ruwa, muka kada kuri’unmu ga Janar, to kuwa ya dace mu kara sadaukar da kai, mu ba shi goyon baya domin mulkinsa ya yi nasara. Ya zama wajibi mu tsarkake zukatanmu, mu gyara halayenmu, mu koyi bin doka da oda, mu koyi aiki tukuru, mu sanya kishin kasa, mu sanya gaskiya da tsoron Allah wajen gudanar da lamurranmu. Ta haka ne kawai za mu iya ba Janar goyon baya, yadda zai samu damar sauke nauyin da muka dora masa na shugabancin Najeriya.
Ina taya Janar Muhammadu Buhari murna, kuma ina taya shi addu’ar samun nasara. Allah Ya ba shi lafiya da karfin zuciyar tafiyar da mulkinsa cikin nasara da adalci. Allah Ya huwace masa mukarrabai masu adalci da son ci gaba, ta yadda za su taya shi sauke wannan nauyi. Allah Ya tabbatar mana da lafiya da zaman lafiya da karuwar arziki a kasarmu baki daya, amin!
***