Mai yada kanjamau ta hanyar fyade ga ’yan mata ya shiga hannu

’Yan sanda a JiharNasarawa sun kama wani matashi mai dauke da cutar kanjamau da ake zargi ya kware wajen yin fyade ga kananan yara mata a Mararraba da ke karamar Hukumar Karu a jihar. Da yake gabatar da wanda ake zargin ga manema labarai a ofishin bincikan manyan laifuffuka (CID) na Rudunar ’Yan sandan Jihar […]

Mai yada kanjamau ta hanyar fyade ga ’yan mata ya shiga hannu
Mai yada kanjamau ta hanyar fyade ga ’yan mata ya shiga hannu

’Yan sanda a JiharNasarawa sun kama wani matashi mai dauke da cutar kanjamau da ake zargi ya kware wajen yin fyade ga kananan yara mata a Mararraba da ke karamar Hukumar Karu a jihar. Da yake gabatar da wanda ake zargin ga manema labarai a ofishin bincikan manyan laifuffuka (CID) na Rudunar ’Yan sandan Jihar Nasarawa da ke Lafiya, Kakakin ’Yan sandan, ASP Numan Umar Isma’il ya ce wani da ya bukaci a sakaye sunansa ne ya kai kara a ofishin ’yan sanda da ke Mararraba cewa ’yarsa mai kimanin shekara 15 ta bar gida don tallar ruwan leda amma ba ta dawo gida ba har dare. A kan haka ne ma a cewarsa iyayen yarinyar suka soma nemanta a gidajen makwabtansu inda daga bisani aka same ta tsirara a gidan wanda ake zargin mai suna Abubakar Atiku inda daga nan suka sanar da jami’an tsaro aka tsare shi.
A cewar Umar Numan Isma’il binciken da ’yan sandan suka gudanar a kan lamarin ya tabbatar da cewa Abubakar Atiku da ake zargi ya kwace kudin cinikin ruwan da yarinyar ta yi ne inda ya rude ta ta bi shi gidansa cewa zai ba ta kudinta. Ya ce ya ja ta dakinsa a gidan ya yi mata fyade a daren kafin ’yan uwanta suka zo suka cece ta daga hannunsa.
Kakakin ’yan sandan ya ce bayan gwaje-gwaje a asibiti da aka yi wa wanda ake zargin an tabbatar yana dauke da kwayar cutar kanjamau, kuma ya amince cewa ya dade yana yi wa kananan yara mata fyade a yankin.