Mai yatsu 31 ta shiga Kundin Tarihi

…Makwabta na kiranta da mayya   Wata mata mai suna Kumari Nayak, mai shekara 63 da ke garin Odisha a Indiya, ta ce mutanen gari suna tsangwamarta saboda halittar da Allah Ya yi mata na yatsun kafa 19 da yatsun hannu 12. Kumari, ta kafa tarihi sakamakon yatsun da take da su da jimillarsu ya […]

Mai yatsu 31 ta shiga Kundin Tarihi

…Makwabta na kiranta da mayya

 

Wata mata mai suna Kumari Nayak, mai shekara 63 da ke garin Odisha a Indiya, ta ce mutanen gari suna tsangwamarta saboda halittar da Allah Ya yi mata na yatsun kafa 19 da yatsun hannu 12.

Kumari, ta kafa tarihi sakamakon yatsun da take da su da jimillarsu ya kai 31, yayin da jama’a da makwabtanta ke kiranta da mayya.

A yanzu haka dai, Kumari Nayak, tana shirin shiga cikin Kundin Tarihi na duniya (Guinness World Records) saboda karin yatsun da take da su da suka sa take da yatsu 31.

Yatsun Kumari Nayak, sun wuce na wata mai suna Debendra Suthar, wadda ta shiga kundin tarihi sakamakon yawan yatsun kafa 14 da yatsun hannu 14,  jimalla yatsu 28 da hakan ya sa ta zama abar misali a duniya.

Sai dai Kumari, wadda ta fito daga Lardin Ganjam da ke yankin Odisha a kasar Indiya, ta bayyana cewa makwabtanta na kallonta a matsayin mayya.

Kumari, ta ce an haife ta da wannan halittar ce, kuma ba ta da yadda za ta yi saboda ta tashi ne a cikin talauci, sannan yanzu ta kai shekara 63 da wannan larura.

Wadansu makwabtan Kumari makafi suna fada mata cewa, ta yi nesa da su ita mayya ce. “Suna zuwa su same ni a cikin wani yanayi amma ba su taimaka min.An tilasta min zaman cikin daki, ana kallon rayuwata daban, ba kamar ta sauran jama’a ba. Hakkin makwabtaka bai tanadi haka ba,” inji ta.

Wani makwabci da ya san halin da Kumari ke ciki, ya ce “Wannan karamin kauye ne da ya kasance jama’a na fuskantar larurar makanta.”

Wani mai suna Odisha, na daya daga cikin makafin, amma yana daukar Kumari tamkar mayya. Duk da yake na san tana da larurar rashin lafiya, wadansu ba su yarda da irin yanayin da take ciki ba.

“Na tausaya mata sakamakon ba ta iya daukar nauyin larurar da take fama da ita,” inji shi.

Kumari, ta ce ba ta da kudin  da za ta iya daukar nauyin jinyar lalurar da ke damunta, don haka ta yanke shawarar zama a gida kawai.

Daga bisani jami’an gwamnatin Indiya sun samu rahoton halin da Kumari ke ciki, kuma hakan ya sa aka ba ta tallafin gida da fansho, sannan sun wayar da kan makwabtanta kan illar kyamarta.

Daya daga cikin jami’an gwamnatin ya ce, gwamnati ta tallafa wa Kumari ne, bayan ta samu rahoton halin kuncin da take ciki. “Mun ilimantar da makwabtan Kumari, kan su nuna mata so da kauna da nuna musu cewa, Kumari ba mayya ba ce,” inji shi.