Mai yaudarar almajirai da N200 ta sace su a Borno ta shiga hannu
Ta yaudari almajiri da N200 da cewa ya raka wurin sayo musu tufafi
Dubun wata mata mai shekaru 60 ta cika bayan ta yaudari wani almajiri da N200 ta sace shi da wasu kananan yara a Maiduguri, Jihar Borno.
’Yan sanda sun cafke matar ce a hanyarta ta zuwa Legas, bayan ta yi sace almajirai biyu ta wata yarinya mai shekara biyu.
- Kotu ta yanke hukuncin kisa ga Faston da ya kashe yaro ya binne gawar a coci
- Kwanan nan za mu hana yin ‘screenshot’ din tattaunawar mutane — WhatsApp
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Borno, Abdu Umar, ya ce a ranar Laraba matar ta sauka a Maiduguri, inda ta je Kasuwar Monday ta ga kananan yara almajirai suna bara.
“Sai ta kira wani daga cikinsu ta ba shi N200 ta ce mishi ya raka ta zuwa inda za ta saya musu kayan saya.
“Sa’annan ta shiga cikin gari inda ta sace wata karamar yarinya,” wadda mahaifiyarta ke sana’ar sayar da nono a ’Yan Nono da ke unguwar Bulumkutu.
“Da ta je tashar mota, sai ta nemi motar Legas, amma aka shaida mata cewa ai motar ta riga ta tafi.
“Sai ta nemi a ba ta masauki ta zauna zuwa washegari, inda a nan ne ta sake fita ta je ta samo yaro na uku.”
Ya bayyana cewa kama ta ne a tashar motocin Borno Express a ranar Alhamis, 4 ga watan Agusta da muke ciki.