Mai yiwuwa Amodu Shu’aibu ya maye gurbin Stephen Keshi
Hukumar kula da kwallon kafa ta kasa (NFF) ta fara tunanin maye gurbin Koci Stephen Keshi da Amodu Shu’aibu nan ba da dadewa ba.Amodu Shu’aibu dai ya taba yi wa kungiyar koci a ’yan shekarun baya kuma ba su wanye lafiya ba bayan da hukumar ta yi masa korar kare saboda rashin tabuka-abin-a-zo-a-gani.Kafar sadarwar wasanni […]
Hukumar kula da kwallon kafa ta kasa (NFF) ta fara tunanin maye gurbin Koci Stephen Keshi da Amodu Shu’aibu nan ba da dadewa ba.
Amodu Shu’aibu dai ya taba yi wa kungiyar koci a ’yan shekarun baya kuma ba su wanye lafiya ba bayan da hukumar ta yi masa korar kare saboda rashin tabuka-abin-a-zo-a-gani.
Kafar sadarwar wasanni ta KickOffNigeria ta ruwaito cewa baya ga Amodu Shu’aibu, hukumar tana yunkurin daukar Sunday Oliseh a matsayin kocin kungiyar. Yayin da hukumar ke tunanin ba Amosu damar ya horar da kungiyar na dan lokaci, shi kuwa Oliseh ana tunani ne a ba shi damar da zai sa ya horar da kungiyar a tsawon lokaci.
Rahoton ya ce ana sa ran hukumar za ta dauki Amodu Shu’aibu aiki ne na wani dan lokaci kafin ta nemo wanda zai maye gurbinsa na dindindijn.
Idan za a tuna, tun bayan da aka fitar da Najeriya a gasar cin kofin duniya Koci Stephen Keshi ya fara tunanin barin kungiyar zuwa kasar Afirka ta Kudu al’amarin da ya bayyana shi a matsayin cewa kwantaraginsa ta kare da kungiyar kuma ba shi da tabbacin ko hukumar NFF za ta sabunta kwantaragin nasa.