Maidoki ya yi tir da rushe masallaci a Jami’ar Fatakwal

Shugaban Kwamitin Zakka da Wakafi na Jihar Sakkwato Alhaji Lawal Maidoki ya ce rushe masallaci da Hukumar Jami’ar kere-kere da ke Fatakwal a Jihar Ribas abin tir ne kuma hakan ba zai haifar da da mai ido ba. Malam Lawal Maidoki ya bayyana haka ne yi a lokacin da yake kaddamar da wasu kayayyaki da […]

Maidoki ya yi tir da rushe masallaci a Jami’ar Fatakwal
Maidoki ya yi tir da rushe masallaci a Jami’ar Fatakwal

Shugaban Kwamitin Zakka da Wakafi na Jihar Sakkwato Alhaji Lawal Maidoki ya ce rushe masallaci da Hukumar Jami’ar kere-kere da ke Fatakwal a Jihar Ribas abin tir ne kuma hakan ba zai haifar da da mai ido ba.
Malam Lawal Maidoki ya bayyana haka ne yi a lokacin da yake kaddamar da wasu kayayyaki da Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji Aliyu Magatakarda Wamakko ya bayar a matsayin wakafi a harabar sakatariyar karamar Hukumar Sakkwato ta Arewa.
Malam Lawal Maidoki ya kara da cewa “Ya kamata Musulmi da Kiristan kasar nan su lura cewa muna fuskantar kalubale mai yawa kan yadda kasashen duniya suka sanya mu a gaba, cewa dole sai mun yi dokar da ta amince da auren jinsi wanda hakan ya saba wa addinanmu gaba daya. Don haka bai kamata a irin wannan hali wata hukuma ta rusa wurin ibadar wasu mabiya wani addini.”
Dagan an sai ya yaba wa namijin kokari da ’yan majalisar kasar nan ke yi, musamman Shugaban Majalisar Dattawa da yake ta gaya wa duniya ba za su canja ra’ayinsu ba duk da tsoratar da su da ake yi za a yanke huldar difilomasiyya da kasar nan.”
Malam Lawal Maidoki wanda tsohon shugaban Majalisar Matasa Musulmi ta Najeriya ne, ya ce za a raba wa mutum 500 shinkafa da sukari da taliya da gero a karkashin kwamitin.