Maigadi ya daddatsa tsohuwar matarsa saboda kin kwanciya da shi
Wani maigadi da ke a titin masallacin layin Bugaje a unguwar Malali Kaduna mai suna Musa Ahmed Rabi’u ya daddatsa tsohuwar matartsa saboda kawai ya nemi kwanciya da ita ta ki a lokacin da ta ziyarce shi a gidan da yake aiki. Matar mai suna Ramatu Ibrahim a yanzu haka tana kwance ne a wani […]
Wani maigadi da ke a titin masallacin layin Bugaje a unguwar Malali Kaduna mai suna Musa Ahmed Rabi’u ya daddatsa tsohuwar matartsa saboda kawai ya nemi kwanciya da ita ta ki a lokacin da ta ziyarce shi a gidan da yake aiki.
Matar mai suna Ramatu Ibrahim a yanzu haka tana kwance ne a wani asibiti mai zaman kansa da ke a Malali, sanadiyyar muggan raunukan da ke a jikinta.
Aminiya da ta ziyarce asibitin ta ruwaito cewa shi dai wannan miji ya nemi halaka tsohuwar matar tasa ce kasantuwar yadda ya sassare ta da wukar da ke hannunsa, domin kuwa fuska da kafuwanta duk a sare suke.
Ramatu ta bayyana wa Aminiya yadda abin ya faru. Ta ce tsohon mijin nata wanda ta haura watanni bakwai kacal kafin su rabu ya dade yana bugun ta. “Ina zaune ne ranar Talata sai na ji kiransa, inda ya nemi in je wajensa domin mu sasanta aurenmu. Saboda haka a ranar Laraba sai na je wajensa, inda yake aiki kuma shi kadai ne a gidan domin mu tattauna yadda za mu sasanta aurenmu, ko na koma dakina.
“Ni ban yi zargin komai ba, koda na je gidan. Bayan na isa da misalin karfe 10 na safe sai muka tattauna da shi a kan yadda yake matukar son ya ga na koma dakina a matsayin matarsa. Amma da misalin karfe 12 da rabi a lokacin da zan koma gida, bayan mun kammala tattaunawa, na kuma amince zai koma dakina. Sai ya bukaci da in shiga daki domin mu kwanta a matsayin mata da miji. Ni kuma sai na ki na kuma fada masa cewa zai fi dacewa da ya shaida wa ’yan uwana da ke a Mararrabar Jos cewa ya maida ni kafin in kwanta da shi.
“Ga alama wannan abin da na fada masa ne ya fusata shi, inda ya cire rigarsa ya ce da ni zai shiga wunka. Ashe zuwa ya yi ya dauko wuka. Daga nan kawai sai na ji an fara sara ta ta ko’ina. Na kasa ihu ballantana in ce wani abu in banda du’ai kawai da nake yi.
Ta ci gaba da cewa: “Da ya kammala raunata ni sai ya saka rigars ya fice daga cikin gidan, ya kuma mayar da kofa ya rufe. Allah ne kawai Ya taimake ni har na ja jiki zuwa wajen kofar fita gidan. Daga nan masu wucewa suka gan ni cikin jini, kafin aka kirawo ’yan sanda su kuma suka kawo ni asibiti.”
Ta ce dama ya saba dukanta lokacin da suke tare. “Lokacin da muke zama tare da shi ba ya bari na in ziyarci ’yan uwana. Akwai lokacin da yayata ta ziyarce mu, inda ya nuna bai ji dadin zuwanta ba. Har yake tambayata ko na fada mata halin da muke ciki, na ce masa a’a.” Inji ta.
kokarin Aminiya na jin ta bakin jami’in hulda da jama’a na rundunar ’yan sanda, SP Aminu Lawan ya ci tura, kasancewar rashin amsa wayarsa da ya yi.