Maigadi ya datse hannun makiyayi saboda jayayya a kan burtali
Wani maigadi a wata majami’a a Gwarinpa da ke Birnin Tarayya, Abuja ya datse hannun wani yaro makiyayi a ranar Lahadi da ta gabata bayan takaddama da ta kaure a tsakaninsu sakamakon kokarin makiyayin na wucewa da dabbobinsa ta wata hanya da ke kusa da inda mabiyar majami’ar ke ajiye motocinsu. Wasu da suka shaida […]
Wani maigadi a wata majami’a a Gwarinpa da ke Birnin Tarayya, Abuja ya datse hannun wani yaro makiyayi a ranar Lahadi da ta gabata bayan takaddama da ta kaure a tsakaninsu sakamakon kokarin makiyayin na wucewa da dabbobinsa ta wata hanya da ke kusa da inda mabiyar majami’ar ke ajiye motocinsu.
Wasu da suka shaida lamarin, sun shaida wa wakilinmu a shekaranjiya Laraba cewa, da farko bayan da suka fara jayayyar, makiyayin ya bar dabbobin a hannun kanwarsa da suke tare ya koma gefe, amma sai maigadin ya je inda makiyayin yake, ya kwace addar da ke hannunsa ya sare shi a kai da kafa da yatsa kafin ya sare shi a wuyan hannunsa ya guntule.
Wani makanike a kusa da inda lamain ya faru a kusa da dutsen Gwarrinpa, ya ce bayan ganin abin da maigadin ya aikata, wani abokin aikinsu ya garzaya ofishin ’yan sanda na Gwarinpa ya sanar da su, inda ’yan sandan suka zo suka kama wanda ake zargin mai suna Jonathan Isiaka, sannan suka kai makiyayin Babban Asibitin Gwarimpa, daga bisani aka kai shi Asibitin kasa na Abuja inda ya ke jinya a halin yanzu.
Babban Jami’in ’Yan sandan Gwarinpa, C.S.P Joseph Mamman ya tabbata da fauwar lamarin, ya ce sun mika wanda ake zargin ga Rundunar ’Yan sanda ta Abuja don ci gaba da bincike a kan al’amarin.