Maigidana ne silar yin da’awata – Hajiya Rabi’at Sufyan Ahmad

“Mace ta gari, ita ce sila ta zama lafiyaMace ta gari gaishe ki gatar al’ummaMace ta gari sai gidan miji…………….” Ga masu sauraron wa’azi da amsa tambayoyi na Malama Rabi’ah Sufyan Ahmad a kafofin watsa labarai daban-daban kamar rediyo da talabiji na gwannati da masu zaman kansu, sun riga sun saba da jin wadannan baitoci […]

Maigidana ne silar yin da’awata – Hajiya Rabi’at Sufyan Ahmad

“Mace ta gari, ita ce sila ta zama lafiya
Mace ta gari gaishe ki gatar al’umma
Mace ta gari sai gidan miji…………….”

Ga masu sauraron wa’azi da amsa tambayoyi na Malama Rabi’ah Sufyan Ahmad a kafofin watsa labarai daban-daban kamar rediyo da talabiji na gwannati da masu zaman kansu, sun riga sun saba da jin wadannan baitoci a yayin bude  daya daga cikin shirye-shiryensu. Zinariya ta samu tattaunawa kai tsaye da shahararriyar malamar addinin inda suka tabo batutuwa da dama kama daga rayuwarta tun tana karama da fadin tashin da ta sha wajen neman ilimi, da gudanar da harkokin rayuwar gida da ta yin wa’azi da kalubalen da take fuskanta da sauransu. Ku biyo mu ku ji yadda hirarta da Mairo Muhammad Mudi ta kasance.

Takaitacen tarihinki
An haife ni a karamar Hukumar Kura ta Jihar Kano amma rayuwata gaba daya na yi ta ne a Jihar Kaduna. Na yi firamare a Kano, da na fara sakandare a Kano sai na dawo Kaduna na ci gaba a wata makaranta mai suna Salamatu Institute of Islamic Studies da ke Unguwar Mu’azu a Kaduna. Bayan na gama sai na tafi Kwalejin horar da malamai da ke Kaduna. Daga nan sai na wuce jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya inda na samu digiri a fannin Larabci da Turanci.  Alhamdulillah na yi kwasa kwasai da dama a wurare daban-daban kamar a kasashen waje irin su Saudi Arebiya da kuma a nan Nijeriya.  Ina da aure kuma ina samu gudunmuwa sosai daga wurin maigida musamman a game da abin da ya shafi karatuna da kuma gudanar da wa’azuzzuka.

Bayan karatu , kina aiki ne ko sana’a ko kuwa harkar fadakarwa ce kawai kika fuskanta?
Alhamdulillah ni tunda na tashi na ga gidanmu ana karatu irin na allo nima da shi na fara kuma tun kamar ina ‘yar shekara bakwai ake samu muna koyarwa ga saura yara. Zan ce daga wurin na fara harkar da’awah. Kuma na yi karatu ina da aure. Tun karatu na sakandare har kwasakwasai da na yi a waje da aurena na yi su. Kuma duk harkokin da’awah da na kungiyoyi da nake ciki da goyon bayan maigidana ne. Na rike mukamai daban-daban a kungiyoyi daban-daban. Na zauna a karkahin wata kungiya mai suna Muslim Sisters Organization inda na zama sakataren harkokin kudi sannan mai kula da bangaren harkokin makarantrr nazari da firamare na kungiyar. Sannan na yi shekaru goma sha biyu ina jami’ar da’awah ta kungiyar FOMWAN. Na rike shugaba na kungiyoyi kamar FOMWAN da kungiya mata masu da’awah da kungiyar mata wadanda suka karanta harshen Larabci.  Sannan don tallafawa marayu sai muka kafa kungiya don tallafawa marayu da marasa galihu wanda ni ke shaugabanci.   Sannan Alhamdulillah na kirkiro da wata makaranta mai suna Ummuyasir Islamic Academy. A karkashin kungiyar mu muna kula da makarantu ashirin da bakwai da masallatai. Ina wadanan da’awah ta shiga kanyuka don kiran wadanda ba masulmi ba zuwa ga musulunci sannan muna tunatar da musulmi. Ina wannan ina karatu,  alhamdulillah yanzun ma na samu takardun damar shiga makarantu biyu don yin babban digiri a Sudan da Cairo, yanzu haka ina nazarin wanda zan zaba a daya daga cikin makarantun don na tafi.

An san aikin da’awah banda daukar lokaci akwai bukatar kudi, ta wace hanya ce kike samun kudaden zartar da wadanan harkokin?
Alhamdulillah babu wata gwannati ko mutum guda da zan ce yana taimaka mana. Ni dai tunda na taso na duba Allah cikin hukuncinSa har zuwa yau bai ba ni haihuwa ba. Na duba na gani da ma amfanin haihuwa shi ne in ka mutu ka samu mai yi maka addu’a don nema maka gafara, to ko dayake Yayana ya rasu ya bar mani yara kanana su kimanin tara kuma ina da wasu yaran wadanda na musuluntar da iyayensu suka yarda su zauna da ni, ya kasance a gidana ba ni rasa yara kamar ashirin da hudu zuwa da biyar amma duk da haka naga gara in kafa abinda ko da bayan raina zai kasance mani abin lada maigudana. Saboda haka ina aiki a karamar hukuman Igabi a matsayin mai kula da harkokin ilimi, a duk lokacin da na karbi albashina na kan raba kashi uku kashi biyu na aikin da’awah ne kashi daya na rike. Alhamdulillah jama’a tana ganin kokarin da mu ke yi tana ba mu gudumawar tafiyar da wannan aikin. Wadanan sune kadan daga cikin hanyoyin samun kudin shigarmu.

Burinki game da wannan aikin.
Burina shine in ga cewa duk macen da mijinta Ya rasu ko dan da ya rasa mahaifinsa na samar musu abin dogaro da kai. Mukan sanya su a makaranta ko mu tura su wuraren da ake koyon sana’o’in hannu ko kuma su samu aikin yi. Abin na da dan wuya amma Alhamdulillah za ki ga duk abinda muka sa gaba Allah na kama mana.

A matsayinki na mace wane irin kalubale kike fuskanta ganin aikin da’awah da na wa’azi harkar maza ne.
A lokacin da na fara wannan aikin gaskiya ban samu matsala da maigidana ba don shi mutum ne da yake da sha’awar na yi wannan aikin.  Yana karfafa mani gwiwa amma wasu mazajen daga waje sukan same shi suna zuga shi.  Sukan yi masa wadansu irin tambayoyi kamar yaushe nake da lokacinsa?  Wannan ba karamin tayar da mani da hankali yake ba.  Amma a wasu lokuta idan aka kira ni wajen yin wa’azi in na nuna masa na gaji ba na son zuwa, sai ya ce ba lada kike nema ba, me ya sa ba za ki je ba.  A mafi yawan lokuta idan ayyuka suka yi mani yawa, ga karatu ga aikin da’awa maigida ne yake taimaka mini da rubuce-rubuce da kuma wasu ayyukan gida Don wata rana ina tuwo shi kuma yana miya ko yin shara.  A lokacin wasu ma suna zargin cewa ko na mallake shi ne, na fi karfinsa, don haka wai yakamata ya kara aure. To ko bayan ya yi auren ban ga wani canji daga wajensa ba, don ya cigaba da karfafa mini gwiwar cigaba da harkokin yada addinin Islama.  Kuma na gode masa a kan wannan jajircewar da ya yi a kaina.

Me kika yi ki ka sace zunciyarsa?
Ba wani abu bane illa biyayya da kyautawa don na san zaman aure shi ne gaba akan da’awar da nake yi. Saboda haka ina da kyakyawar alaka da maigidana. Wata rana wasu kan yi mamaki in sun zo gidanmu sun tarar ina masa waka da rawa ko muna buga kwallo muna yin guje-guje da shi.

Kullum a kan ganki cikin hijabi daga kai har kafa,  yaya zance yi wa maigida kwalliya?
A gaskiya sai mutum ya zo gidana ne zai ga yadda nake yi wa maigidana kwalliya. Na kan sa sutura irin su siket da dogon wando ko gajere ko kuma karamar riga ta shan iska. Wata rana in yi kitso ko na bar gashina a kwance don ya yi sha’awa. Nakan shafa turare mai kamshi da na san in ya shigo zai jawo hankalinsa don ya kalle ni. Wasu matan da