Maimuna S. Beli ce ta lashe gasar Hikayata na BBC
Maimuna S. Beli, yar asalin Jihar Kano ce ta lashe gasar rubutun kajerun labarai wande ake kira Hikayata ta bana wanda BBC ke shiryawa. Maimuna dai ta samu damar lashe gasar ne da labarinta mai suna “Bai Kai Zuci Ba”, inda ta bayyana yadda wata mata ta dimauce da son ‘ya’yanta, har ya kai ga […]
Maimuna S. Beli, yar asalin Jihar Kano ce ta lashe gasar rubutun kajerun labarai wande ake kira Hikayata ta bana wanda BBC ke shiryawa.
Maimuna dai ta samu damar lashe gasar ne da labarinta mai suna “Bai Kai Zuci Ba”, inda ta bayyana yadda wata mata ta dimauce da son ‘ya’yanta, har ya kai ga tana tunanin ko ya ‘ya’yan za su kasance idan ta mutu, hakan ya sa ta umarci maigidanta ya auri kawarta, saboda ta lura kawar na son yara.
Za ayi gagarumin biki na musamman a ranar Juma’a, 24 ga watan Nuwanba domin karrama Maimuna S. Beli, da wadanda suka zo na biyu da na uku a Abuja.