Maimuna Y. Abubakar: Yadda nake hada aikin lauya da buga mujalla

Maimuna Y. Abubakar lauya ce kuma Babbar-Editar Mujallar Tozali da ke Abuja. Ta yi bayanin dalilin da ya sa ta kirkiro Mujallar Tozali da yadda take hada aikin lauya da kuma buga mujallar. Tarihina a takaiceAssalamu alaikum, sunana Maimuna Yaya Abubakar daga Jihar Gombe. Na yi makarantar Sakandaren ‘Yan Mata ta Tarayya da ke Bauchi. […]

Maimuna Y. Abubakar: Yadda nake hada aikin lauya da buga mujalla

Maimuna Y. Abubakar lauya ce kuma Babbar-Editar Mujallar Tozali da ke Abuja. Ta yi bayanin dalilin da ya sa ta kirkiro Mujallar Tozali da yadda take hada aikin lauya da kuma buga mujallar.

Tarihina a takaice
Assalamu alaikum, sunana Maimuna Yaya Abubakar daga Jihar Gombe. Na yi makarantar Sakandaren ‘Yan Mata ta Tarayya da ke Bauchi. Na  kuma yi karatun Lauya a Jami’ar Bayero da ke Kano, kafin na je makarantar zama lauya a Legas, wato Law School ke nan. Daga nan na fara aiki a Hukumar yi wa Kamfanoni Rajista (CAC) na tsawon shekara hudu, inda na rike mukamin Mataimakiyar Manaja. Daga nan na daina aiki, inda na zama lauya mai zaman kanta. Ko lokacin da nake aiki na koma makaranta inda na yi digiri na biyu a kwas din Huldar Kasuwanci. Daga baya sai na kafa Mujallar Tozali, inda a yanzu shekara shida ke nan. Duk da haka ban daina aikin lauya mai zaman kanta ba.
Hada aikin lauya da buga Mujallar Tozali
Lokacin da na fara Mujallar Tozali ba ni da kudi a kasa, hakan ya sanya dole na nemi kudin da zan buga mujallar, kasancewar ina da burin kafa mujalla tun ina makarantar sakandare, dangane da aikin lauya kuma idan ka yi kamar ayyuka biyu zuwa uku za su iya rike ka zuwa wani lokaci kamar wata daya ko biyu ko fin haka ma. Don haka bayan na bar aiki sai na ga ba ni da kudin da zan iya buga mujallar, hakan ya sa na ce bari in raba kafa; ga aikin lauya ga kuma buga mujallar. Cikin ikon Allah ina fara aikin lauya sai na hadu da mutane, inda na rika samun aiki kuma kudi ya rika shigowa, sai na rika zuba kudin da na samu a Mujallar Tozali.
Sannu-a-hankali dai har Mujallar tsaya da kafafunta, wato ta kama wa kanta ofis, ta samu kudin da take biyan ma’aikata, ta buga kanta da sauransu. Wani lokaci har a samu kudin da ake saya mata kadara ko a ajiye mata saboda gaba.
Yadda nake taimaka wa mata
Ba wai kawai aikin lauya ba, idan za ka duba Mujallar Tozali an yi ta don mata ne, kuma don ta fito da matan arewa, saboda babu wata mujallar da ta yi wa matan arewa wannan gatan, musamman idan aka je kudu za a ga mujallun mata masu yawa, kuma burinsu su fito da matan yankinsu. A Tozali za a ga kowace fitowa akwai shafukan girke-girke, hira da wata tauraruwa daga yankin arewa, wanda hakan zai sa wadansu mata daga yankin su ji cewa idan suka jajirce za su iya taka babban matsayi. Bayan haka akwai bikin da muke yi mai suna Tozali Henna Ball Award duk bayan shekara biyu. An kirkiro bikin ne don a tara kudin da za a taimaka wa yara mata ta fannin karatu da sana’a da sauransu. Mukan duba iyalan da suke da bukata wadanda za ka samu ’ya’yansu suna da hazaka, amma babu wanda zai dauki nauyin karatunsu. Mukan biya musu kudin makaranta lokaci zuwa lokaci, ba kuma muna yi musu alkawarin daukar nauyin karatun na dindindin ba ne. Muna taimakawa iya yadda za mu iya. Mukan je kauyuka mu wayar da kan iyaye a kan muhimmancin ilimi ga ‘ya’yansu, wani lokaci mu ba iyaye kudin da za su sa ’ya’yansu a makaranta, sannan mukan saya wa matan aure marasa aikin yi firij su rika sayar da kankara ko mu saya musu keken dinki ko dai wani abu da za su rika taimaka wa kansu.

Halayen da na koya a wurin iyayena
Iyayena sun gargade ni kada in raina kowa, mutum komai kankantarsa ko talaucinsa, to in ba shi daraja. Kada in rika nuna dagawa ko izza da kasaita. Mahaifiyata ta koya mini in rika yin sana’a ko wani abu da zai taimake ni a rayuwa. Na taso na ga mahaifiyata tana aiki a karkashin Hukumar NEPA tun kafin ta zama PHCN, bayan ta haife ni ne ta daina aiki, sai ta fara wadansu ayyuka, inda ta yi kiwon kaji, ta koya wa mata yadda ake yin sabulu. Don haka mahaifiyarmu ba ta so danta ya zauna ba tare da yin wani abu da zai taimake shi, ko ya taimaki al’umma ba.
Mahaifina aikin gwamnati ya yi har zuwa ritaya, ya nuna mini muhimmancin karatu. Mu takwas ne a gidanmu kowa ya yi karatu, idan ban da daya da yake jami’a dukkanmu ribar karatun muke ci. Na samu kyakkyawar tarbiyya a gida, shi ya sa ma suka ba ni dukkan gudunmuwar da nake bukata wajen buga mujallar Tozali da kuma aikin lauya, domin sun gamsu da irin tarbiyyar da suka ba ni.
kalubale a rayuwa
Na fuskanci kalubale sosai, kamar yadda na gaya maka a baya ne, ko lokacin da na fara Mujallar Tozali ai ba ni da kudi a kasa, hakan ya sanya na fara da kadan, ban kinkimo abin da ya fi karfina ba, inda na fara da kwafi dubu, ba tare da bugu mai inganci ba, sannu-a-hankali muka rika bugawa da yawa; muka kuma samar da bugu mai inganci.
Daga farko kamar na rika dibar kudina ina zubawa a rami ne. Haka za a je da Tozali kasuwa a dawo da ita babu wanda ya saya, aka yi bugu na daya da na biyu har zuwa na biyar. Na rika zama da masu sayar da mujallar don a gano bakin zaren, da haka dai har jama’a suka rika saya.
kalubale na biyu da na fuskanta shi ne, samun wakilai da kwararren edita, inda mujallar ta rika fitowa da kura-kurai masu muni. Daga baya muka fuskanci matsalar rabawa, sai kuma rashin samun talla, wanda ya sanya na ce ba dole sai da talla ba, me zai hana mu nemo wata hanya, hakan ya sanya daga baya na kawo batun sanya hotunan aure, a nan ne na lura idan har an sanya hotunan aure sai ka ga Tozali ta kare har ana nema, a yanzu ta kai idan ba a sanya hotunan auren mutum a Tozali ba, to bai hadu ba.
Shawara ga mata
Ya kamata mata su rika yin wata sana’a don su dogara da kansu, a halin yanzu ana cikin talauci, ba komai ne mata za ta jira sai mijinta ya kawo mata ba, ya kamata mata su tashi. Idan sun yi hakan ba sai sun jira miji ya kawo kudin magi da gishiri ba. Wani lokaci sai ka ga an koro yara saboda kudin islamiyya, amma idan aka ce mata na yin wata sana’a, ba sai sun jira miji ya dawo ba za su bayar. Ya kamata idan mata sun fita nema, to su bi yadda shari’a ta tanada. Baya ga haka idan mata suna sana’a za su taimaka wa ’yan uwa da abokan arziki.