Maiyiwuwa Cristiano Ronaldo ya fuskanci hukunci
Shugaban Hukumar kwallon kafa ta Sifen Jabier Tebas ya ce akwai yiwuwar Hukumarsa ta hukunta shahararren dan kwallon kulob din Real Madrid Cristiano Ronaldo a bisa zarginsa da cin mutuncin magoya bayan kulob din FC Barcelona na Sifen jim kadan bayan ya zura kwallo a ragar FC Barcelona a ranar Lahadin da ta wuce. Cristiano […]
Shugaban Hukumar kwallon kafa ta Sifen Jabier Tebas ya ce akwai yiwuwar Hukumarsa ta hukunta shahararren dan kwallon kulob din Real Madrid Cristiano Ronaldo a bisa zarginsa da cin mutuncin magoya bayan kulob din FC Barcelona na Sifen jim kadan bayan ya zura kwallo a ragar FC Barcelona a ranar Lahadin da ta wuce.
Cristiano Ronaldo dai ya rika yi wa magoya bayan kulob din Barcelona shagube da hannayensa ina yake nuna cewa “su kwantar da hankalinsu”.
Hakan ta sa shugaban hukumar ya ce, hukumarsa ba za ta amince da irin wannan halin da ka iya harzuka magoya baya wajen kawo rudani da kuma tashin hankali a filin kwallo ba.
Shugaban ya ce abin da Ronaldo ya yi ya saba wa ka’ida, kuma zai yi duk mai yiwuwa don ganin an hukunta dan kwallon don ya zama darasi ga na-baya.
Idan hukuncin ya tabbata, akwai yiwuwar a dage dan kwallo a wasa daya ko biyu ko uku a gasar ta La-Liga.
Idan kuma aka yi masa sassauci watakila a ci tararsa wajen biyan kudi ne ba tare da an dage shi daga yin wasa ba.