Maizabura ya bukaci ’yan majalisa su yi koyi da Buhari

Wani tsohon dan siyasa Alhaji Umar Muhammad Maizabura, ya bukaci ’yan Majalisar Dattawa da ta Wakilai su mayar da hankalin wajen yi wa talakawa aiki don ci gaban kasa, kamar yadda Shugaba Buhari yake yi.Alhaji Umar Maizbura ya bayyana haka ne a Maiduguri lokacin da yake tattaunawa da Aminiya, inda ya ce matukar ’yan majalisar […]

Maizabura ya bukaci ’yan majalisa su yi koyi da Buhari
Maizabura ya bukaci ’yan majalisa su yi koyi da Buhari

Wani tsohon dan siyasa Alhaji Umar Muhammad Maizabura, ya bukaci ’yan Majalisar Dattawa da ta Wakilai su mayar da hankalin wajen yi wa talakawa aiki don ci gaban kasa, kamar yadda Shugaba Buhari yake yi.
Alhaji Umar Maizbura ya bayyana haka ne a Maiduguri lokacin da yake tattaunawa da Aminiya, inda ya ce matukar ’yan majalisar suka rarraba kawunasu ko suka ki bai wa Shugaban kasa hadin kai game da ayyukan da ya sanya a gaba, za a iya samun nakasu ga ci gaban tattalin arziki, kuma komai zai iya tsayawa a kasar nan.
Ya ce jayayya ko jan kafa a kan kasafin kudi da sauran kudirorin da Shugaban kasa ya mika wa majalisa ba abu ne da zai kai ga kasar nan ga tudun mun-tsira ba. Ya ce wajibi ne ’yan majalisa su san cewa yi wa kasa hidima ne ya kai su majalisar ba neman azurta kai da barnata dukiya ba. Maizabura ya ce akwai ’yan majalisar da suka dauke ta a matsayin wurin kawo ci gaban kasa, kuma takaddama a tsakanin bangaren zartarwa da na majalisa akan yi ne don kawo ci gaba.
“Yanzu dai an daidaita a tsakanin bangaren zartarwa da na majalisa kan kasafin kudin bana har an sanya hannu, to amma akwai bukatar ’yan majalisar su rika duba mutanen da suka zabe su don su je su yi musu aiki ta hanyar hada kai da bangaren Shugaban kasa, kafin su yi tunanin cin
ribar abin da suka kashe a wajen yakin neman zabe. Don haka su mayar da hankali wajen yi mana aiki domin mu samu ci gaba,” inji shi.
Maizabura, ya bukaci ’yan Najeriya su ci gaba da juriya da hakuri kan matsin tattalin arzikin da ake fama da shi, inda ya ce nesa ta zo kusa, ganin yadda Shugaba Buhari ya tashi haikan yana nemo bakin zaren matsatalar. “Ya kamata mutane su gane cewa barna ce ba ta da wahala, amma kafin a shawo kan barnar da aka tafka shekara 16, ba kankanen lokaci za a dauka ba. Abin da ya rage kawai ga ’yan Najeriya shi ne su ta addu’a ga Shugaba Buhari tare da yin hakuri a kan yadda aka tsinci kai,” inji shi.