Majalisa amince wa Tinubu ciyo bashin $500m don sayen mitocin lantarki

Tinubu zai ciyo bashin Dala miliyan 500 daga Bankin Duniya don sayo mitocin wutar lantarki ga ’yan Najeriya

Majalisa amince wa Tinubu ciyo bashin $500m don sayen mitocin lantarki

Majalisar Dattawa ta sahale wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ciyo bashin Dala miliyan 500 da nufin samar da mitocin wutar lantarki ga ’yan Najeriya.

A zaman majalisar na ranar Labara ne ta amince wa Shugaba Bola Tinubu ya karbo bashin daga Bankin Duniya.

Bayan karbar rahoton kwamitin basukan kasashen waje ne majalisar ta amince da karbo bashin wanda za a damka ga Hukumar Kula da Kamfanonin Gwamnati (BPE).

Bashin Dala miliyan 500 da za a sayi mitocin lantarkin da su wani bangare ne na bashin  Bankin Duniya na Dala biliyan 7.94 da Tinubu ya samu anincewar majalisar da zai karbo a karkashin tsarin karbar basukan kasashen waje na 2022-2024.

Da yake gabatar da rahoton, mataimakin shugaban kwamitin, Sanata Haruna Manu, ya ce kudaden da mitocin za su taimaka wajen ingata samun wutar lantarki a kasar.

A cewarsa, aikin samar da mitocin zai kara ingantar karfin kamfanonin rarraba wutar lantarki da kuma samun kudaden shiga a gare su.

Kirsimeti: FRSC ta aike jami’ai 1,539 zuwa Kano

Gwamnatin Kano na shirin tara harajin 80bn a 2025

Kirsimeti: Zulum ya ɗauki nauyin jigilar fasinjoji 710 zuwa garuruwansu

Ɗan shekara 60 ya rasu a hatsarin kwalekwale a Sakkwato