Majalisa na bincikar NNPC kan Dala biliyan 1.05

Majalisar Wakilai na bincikar kamfanin mai na NNPC a kan zargin cirar Dala biliyan 1.05 daga ribar iskar gasa ba bisa ka’ida ba. Majalisar ta bukaci shugabannin kamfanin NNPC da kuma kamfanin iskar gas na kasa (NLNG) su bayyana a gabanta domin amsa tambayoyi kan kudaden. Buhari ya mika wa majalisa sunan sabbin alkalai 11 […]

Majalisa na bincikar NNPC kan Dala biliyan 1.05

Majalisar Wakilai na bincikar kamfanin mai na NNPC a kan zargin cirar Dala biliyan 1.05 daga ribar iskar gasa ba bisa ka’ida ba.

Majalisar ta bukaci shugabannin kamfanin NNPC da kuma kamfanin iskar gas na kasa (NLNG) su bayyana a gabanta domin amsa tambayoyi kan kudaden.

Maganar ta taso ne sakamakon kudurin da Shugaban Marasa Rinjaye, Ndudi Elumelu (PDP, Delta), ya gabatar.

Elumelu ya zargi NNPC da yin gaban kansa ba tare da tuntubar majalisa ba wajen cirar Dala biliyan 1.05 daga asusun ribar NLNG, sabanin abin da doka ta tanada.

Dokar ta yi tanadi cewa NNPC, wanda ke wakiltar Gwamantin Tarayya a Kwamitin Amintattu na NLNG ba zai ciri kudi daga asusun ba sai da amincewar majalisa.

Zauren majalisar ya umarci kwamitinsa na asusun gwamnati ya gayyanci NNPC da NLNG, domin yin cikakken bincike a kan kudaden iskar gas, sannan ya gabatar masa da rahoto a cikin mako hudu.

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno