Majalisa na ci gaba da tantance sauran Ministoci

A jiya Laraba da Majalisar dattawa ta fara tantance Ministoci, inda aka tantance mutum goma daga cikin sunaye 43 da ake saran zasu rike mukaman Ministoci. A yanzu haka ana ci gaba da tantance sauran Ministocin, kuma majalisar na saran a yau Alhamis zata tantance sunaye takwas da suka hada: Bashir Salihi Magashi (Kano), Timipre […]

Majalisa na ci gaba da tantance sauran Ministoci

A jiya Laraba da Majalisar dattawa ta fara tantance Ministoci, inda aka tantance mutum goma daga cikin sunaye 43 da ake saran zasu rike mukaman Ministoci.

A yanzu haka ana ci gaba da tantance sauran Ministocin, kuma majalisar na saran a yau Alhamis zata tantance sunaye takwas da suka hada:

Bashir Salihi Magashi (Kano), Timipre Sylva (Bayelsa), Richard Adeniyi Adebayo (Ekiti), Mustapha Baba Shehuri (Borno), Ramatu Tijjani (Kogi), Mohammed Abdullahi (Nasarawa), Tayo Alasoadura (Ondo)  da Sunday Dare (Oyo).

Wadanda aka tantance a jiya sun hada da;

1.Uchechukwu Ogah (Abia)
2.Goodwill Akpabio (Akwa Ibom)
3.George Akume (Benue)
4.Ogbonnaya Onu (Ebonyi)
5.Emeka Nwajuaba (Imo),
6.Olorunnimbe Mamora (Lagos)
7.Olamilekan Adegbite (Ogun)
8.Adamu Adamu ( Bauchi)
9.Rotimi Amaechi .(Rivers)
10. Sharon Ikeazor (Anambra).