Majalisa Na Neman Ministan Lafiya Kan Badaƙalar Dala Miliyan 300
Tun shekarar 2021 aka tanadi kuɗin domin yaƙi da cutar maleriya ta zazzabin cizon sauro.
Kwamitin Majalisar Wakilai kan yaƙi da cutar maleriya da kanjamau da tarin fuka, na neman Ministan Lafiya, Farfesa Muhammad Ali Pate da ya bayyana a gabanta kan zargin almundahanar dala miliyan 300.
Ministan tare da sakatariyar ma’aikatar, Daju Kachollom za su bayyana a gaban majalisar ne bisa zargin karkatar da maƙudan kuɗin da aka tanada domin yakar cutar maleriya tun a shekara 2021.
- Za mu raba wa jami’an tsaro tallafin abinci — Gwamnan Kano
- Majalisa ta ba da wa’adin nemo ɓata-garin da suka kashe sojoji a Delta
Shugaban kwamitin, Amobi Godwin Ogah ya kuma ce mutanen biyu za su ba da bahasi kan wani zargin da ake yi musu na hana masana’antun cikin gida kwantiragin samar da gidajen sauro masu magani da sauran kayayyaki.
A cewar shugaban kwamitin, a shirye suke su sanya a kamo sakatariyar bisa kin amsa gayyatar majalisar da ta yi har sau uku a jere.
Aminiya ta rawito cewa, Ogah ya ce gwamnatin Najeriya a shirye take ta tallafa wa al’umma, sai dai ma’aikatan farar hula a kullum su ke kawo mata cikas.
“An samar da kudin nan tun a 2021, kuma mun sha gayyatar sakatariyar ma’aikatar amma shiru kake ji.
“Abin da muke son ji shi ne shin sun yi amfani da kuɗin nan? Idan ba su yi ba ina suke?
“Amma sai kauce-kauce suke ta yi. Sai dai wannan ba zai kashe mana guiwa ba. ‘Yan Najeriya sun zaɓe mu ne domin mu wakilce su, don haka ba za mu bari larurar maleriya ta ci gaba da kashe su ba.
“Gwamnati na ta kokarin ganin hakan ya samu daga nan zuwa shekarar 2030.
Kazalika, Ogah ya ce majalisar ta bai wa ministan da sakatariyarsa wa’adin sa’o’i 72 domin gabatar da kansu a gaban kwamitin, ko su fuskanci fushinsu.